Delta: An Sanar da Zaben Kananan Hukumomi, Ƴan Adawa Sun Lashe Kujera

Delta: An Sanar da Zaben Kananan Hukumomi, Ƴan Adawa Sun Lashe Kujera

  • Hukumar zabe a jihar Delta ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 25 da aka gudanar a jiya Asabar
  • Hukumar ta tabbatar da cewa jami'yyar PDP ta lashe duka zaben da aka gudanar a ƙananan hukumomi 25 a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024
  • A zaben kansiloli kuma, PDP tayi nasara a unguwanni 499 yayin da jam'iyyar APM ta samu kujera daya ta kansila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Hukumar zabe a jihar Delta ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar.

Hukumar ta ce jam'iyyar PDP ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 25 a zaben.

Kara karanta wannan

Adamawa: NNPP ta lashe kujera 1 yayin da aka sanar da zaben kananan hukumomi

PDP ta lashe zabukan kananan hukumomi 25 a Delta
Jami'yyar PDP ta yi nasara a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Delta. Hoto: Sheriff Oborevwori.
Asali: Facebook

Delta: PDP ta lashe zaben kananan hukumomi

Shugaban Hukumar zabe a jihar Delta, Jerry Agbaike shi ya tabbatar da haka a yau a Lahadi 14 ga watan Yulin 2024, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerry ya ce daga cikin ƴan takarar akwai wanda ba shi da abokin hamayya a zaben da aka gudanar a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024, Punch ta tattaro.

Hukumar ta ce ba a gudanar da zabe a karamar hukumar Udu ba saboda dan takarar jam’iyyar PDP, Vincent Oyibode ba shi da abokin hamayya.

Jam'iyyar APM ta samu kujerar kansila 1

A zaben kansiloli kuwa, PDP ta lashe unguwanni 499 da aka yi zabe yayin da jam'iyyar APM ta lashe kujerar kansila daya.

Jam'iyyar APM ta yi nasara ne a wata unguwa da ke karamar hukumar Oshimili ta Arewa da ke jihar.

Kara karanta wannan

Rugujewar gini kan dalibai: Gwamnatin Filato ta sanar da ranakun zaman makoki

Gwamna Sheriff Oborevwori zai rantsar da shugabannin kananan hukumomi 25 din a gobe Litinin 15 ga watan Yulin 2024.

An sanar da sakamakon zabe a Adamawa

Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta lashe duka zabukan da aka gudanar na kananan hukumomi 21 a jihar Adamawa.

Hukumar zabe a jihar ita ta tabbatar da haka inda ta ce an kuma gudanar da zabukan kansiloli a jihar a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024

Jam'iyyar NNPP mai adawa a jihar ta yi nasarar lashe kujerar kansila daya a karamar hukumar Demsa da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.