APC Ta Yi Babban Kamu, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Koma Jam'iyyar
- Jam'iyyar APC ta samu ƙaruwa bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim ya koma cikinta
- Tsohon shugaban na majalisar dattawa ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC ne yayin wani taron yaƙin neman zaɓe a jihar Ebonyi
- Ya samu tarba daga manyan jiga-jigan jam'iyyar da suka haɗa da Abdullahi Umar Ganduje da gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Ya bayyana komawa APC ne a filin wasa na Pa Oruta Ngele da ke Abakaliki a yayin babban taron yaƙin neman zaɓen ƙananan hukumomi na jam’iyyar APC a ranar Asabar.
Sanata Anyim ya koma APC
Ya jagoranci jiga-jigan fitattun mutane daga sauran jam’iyyun siyasa da suka hada da tsofaffin ƴan majalisar jiha da na tarayya zuwa jam'iyyar APC, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin jiga-jigan ƴan siyasan da ya jagoranta zuwa APC akwai tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP, Edwin Nkwegu, Sanata Obinna Ọgba, tsofaffin ƴan takarar majalisar tarayya da jiha da dubban magoya bayansu.
A wajen tarbarsu akwai shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Gwamna Hope Uzodinma, gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Sauran sun haɗa da ministan ayyuka, David Umahi, shugaban jam’iyyar APC na jihar Ebonyi, Stanley Meghan da sauran jiga-jigan jam'iyyar.
Da yake jawabi a wajen taron, ministan ayyuka, David Umahi ya yabawa Anyim bisa goyon bayan da ya ba APC a zaɓen 2023 inda ya ƙara da cewa takwas ya yi daidai da ya koma jam’iyyar.
David Umahi ya godewa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan goyon bayan ya ba shi a lokacin da ya fuskanci ƙalubalen shari’a bayan ya koma jam’iyyar APC.
Tsohon sanata ya fice daga APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan APC a Kano, Sanata Mas'ud Doguwa ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa Peoples Democratic Party (PDP).
Masud Doguwa ya koma jam'iyyar PDP ne bayan ya zargi gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da cewa ba ta da alƙibla.
Asali: Legit.ng