Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci a Ƙarar da Aka Nemi Tsige Gwamnan PDP
- Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan ƙarar da LP da ɗan takararta na gwamna suka kalubalanci sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa
- Alkalan kotun sun amince da hukuncin kotun sauraron kararraƙin zaɓe wadda ta kori ƙarar bisa rashin cancanta
- Jam'iyyar LP da Udengmobofa Eradiri sun yi zargin cewa Gwamna Diri da mataimakinsa sun yi amfani da takardun bogi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa - Kotun ɗaukaka ƙara ta kori karar da jam'iyyar LP da ɗan takararta na gwamna suka ƙalubalanci nasarar Gwamma Douye Diri na jihar Bayelsa.
LP da ɗan takararta na gwamna, Udengmobofa Eradiri sun ƙalubalanci matakain hukumar zaɓe INEC na ayyana Gwamna Diri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a watan Nuwamba, 2023.
Kwamitin alƙalai uku na kotun ɗaukaka ƙara ya yanke cewa kotun zaɓe tana da gaskiya da ta kori ƙarar LP bisa rashin cancanta, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta kori ƙarar LP
Kotun ta ce Mista Eraɗiri da jam'iyyarsa sun gaza gabatar da hujjojin da za su gamsar da ita kan zargin rashin cancanta da takardun bogi da suke wa Diri da mataimakinsa.
Haka nan kuma kotun ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin kotun zaɓe wadda ta yanke cewa masu shigar da ƙara sun yi watsi da shari'ar.
Ta ce babu sa hannun masu shigar da ƙara ko lauyoyinsu a takardar ƙarar kamar yadda doka ta tanada, wanda ke nuni da ba su ɗauki shari'ar da muhimmanci ba.
Kotu ta ci tarar LP da Eradiri
Dangane da batun jabun takardu da LP ta yi ƙorafi, kotun ta ce lamari ne da ya shafi harkokin gabanin zaɓe wanda kwata-kwata bai kamata a taso da shi a yanzu ba.
Daga ƙarshe alƙalan sun ci tarar masu ƙara tare umartar su baiwa kowane ɗaya daga cikin waɗanda suke ƙara N200,000, Tribune Online ta tattaro.
Kwankwaso ya kaddamar da tambarin NNPP
A wani rahoton kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya ce sabon tambarin NNPP zai bayyana a takardun kaɗa kuri'a a zaɓen gwamnan Ondo.
Jagoran NNPP na ƙasa ya ce sun ɗauki matakin canza tambarin ne bisa la'akari da ƙalubalen da jam'iyyar ta fuskanta a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng