Kwankwaso Ya Faɗi Jihar da Za Ta Fara Amfani da Sabon Tambarin NNPP a Najeriya
- Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya ce sabon tambarin NNPP zai bayyana a takardun kaɗa kuri'a a zaɓen gwamnan Ondo
- Jagoran NNPP na ƙasa ya ce sun ɗauki matakin canza tambarin ne bisa la'akari da ƙalubalen da jam'iyyar ta fuskanta a zaɓen 2023
- Kwankwaso ya kaddamar da sabon tambarin a wani taro da mambobin NNPP suka gudanar a birnin tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jagoran New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya ce sabon tambarin jam'iyyar zai fara aiki a zaɓen gwamnan Ondo.
Idan baku manta ba a zaben da ya gabata NNPP ta fuskanci matsaloli sakamakon tambarin da ta ke da shi a baya, wanda a yanzu aka sauya shi cikin salo mai kayatarwa.
Yayin wani taro da ‘ya’yan jam’iyyar NNPP suka yi a Abuja, Injiniya Kwankwaso ya ƙaddamar da sabon tambarin mai ɗauke da hoton littafi da hular karatu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma jaddada cewa sabon taken NNPP watau “Ilimi ga kowa” ya ƙara fito da kudirin jam'iyyar na samar da ilimi mai inganci da tallafawa talaka, Leadership ta ruwaito.
Meyasa NNPP ta canza tambari?
Kwankwaso ya bayyana cewa gaba ɗaya ƴaƴan NNPP sun amince da shawarar canza tsohon tambarin da ke dauke da kwandon kayan marmari.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya kuma yi bayanin cewa tsohon tambarin da ke ɗauke da kwandon kayan marmari ya jawo wa jam'iyyar NNPP matsaloli a zaɓen da ya wuce.
A cewarsa, sakamakom rashin bayyanar tsohon tambarin ɓaro-baro a takardar kaɗa kuri'a, jam'iyyar NNPP tayi asarar ɗumbin ƙuri'u a zaɓen 2023.
Bugu da ƙari, ya ce tsohon tambarin ya haifar da ruɗani a tsakanin masu kaɗa kuri'a, wanda bisa wannan dalili ya sa suka ga ya dace su canza shi zuwa na yanzu.
Wani mamban NNPP, Malam Sa'idu Abdu ya shaidawa Legit Hausa cewa dama ya kamata a sauya tambarin jam'iyyar wanda suke zargin ya kawo masu nakasu a zaɓen 2023.
"Wannan ci gaba ne da muka daɗe muna jira saboda abubuwan da suka faru a zaben da ya wuce, mutane ba su iya tantance NNPP a takardun ƙuri'u ba.
"Muna fatan wannan sabon ya warware matsalar da aka samu a baya," in ji shi.
APC ta gamu da cikas a jihar Edo
A wani rahoton kuma Tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon Pally Iriase ya yi fatali da naɗin da APC ta masa a matsayin mamban kwamitin kamfe a Edo.
Iriase ya bayyana cewa babu wanda ya tuntuɓe shi gabanin sanya sunansa kuma tun da jimawa ya jingine harkokin siyasa.
Asali: Legit.ng