Ganduje Ya Gamu da Matsala, Ɗan Majalisa Ya Yi Fatali da Naɗin da Aka Masa a APC
- Tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon Pally Iriase ya yi fatali da naɗin da APC ta masa a matsayin mamban kwamitin kamfe a Edo
- Iriase ya bayyana cewa babu wanda ya tuntuɓe shi gabanin sanya sunansa kuma tun da jimawa ya jingine harkokin siyasa
- A ranar Laraba, jam'iyyar APC ta ƙasa ta fitar da jerin mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamna a Edo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - All Progressives Congress (APC) ta gamu da cikas yayin da take shirye-shiryen tunkarar zaɓen gwamnan jihar Edo mai zuwa a 2024.
A ranar Laraba jam'iyyar APC ta fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓe a jihar Edo a ƙoƙarinta na kwace mulki daga hannun PDP.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon Pally Iriase, wanda yana ɗaya daga cikin mambobin kwamitin kamfen APC, ya yi fatali da muƙamin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Hon Iriase ya ƙi shiga kamfen APC?
Sunan Iriase na cikin jerin ƴan kwamitin kamfen to amma a wata sanarwa da ya fitar da yammacin Jumu'a, ya ce babu wanda ya tuntuɓe shi gabanin sa sunansa.
Ya kuma bayyana cewa tuni ya jingine harkokin siyasa a rayuwarsa don haka ba zai shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC ba.
Honorabul Iriase, tsohon mataimakin mai tsawatarwa a majalisar wakilai ta ƙasa ya godewa APC ta ƙasa bisa ganin ya dace ya shiga kwamitin kamfe a jihar Edo.
Tsohom ɗan majalisar ya godewa APC
A kalamansa ya ce:
"An jawo hankalina kan cewa sunana ya shiga cikin jerin sunayen wadanda aka nada a kwamitin Kamfen jam'iyyar APC na zaben gwamnan jihar Edo
"Na godewa kwamitin gudanarwa NWC na APC ta ƙasa bisa ganin na dace da shiga kwamitin, amma ina bada haƙurin cewa ba zan karɓi naɗin ba saboda dalilai.
"Na farko babu wanda ya tuntuɓe ni, sannan na biyu na riga na yanke jimgine siyasa shekaru da dama da suka wuce kuma bani da niyyar sauya matsaya ta."
A ƙarshe ya yi wa jam'iyyar APC fatan samun nasara a kamfen da ta tasa a gaba tare da rokon jam'iyyar ta girmama matakin da ya ɗauka, Leadership ta ruwaito.
Zaɓen Edo: PDP ta ɗaukaka ƙara
A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ba ta gamsu da hukuncin babbar kotun tarayya ba na soke zaɓenn fidda gwaninta na gwamnan jihar Edo
PDP ta ɗaukaka ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja domin nuna adawa da hukuncin na soke takarar Asue Ighodalo.
Asali: Legit.ng