Dan Majalisar Tarayya a Kano Ya Soki Mataimakin Kakakin Majalisa, Ya Ci Gyaransa

Dan Majalisar Tarayya a Kano Ya Soki Mataimakin Kakakin Majalisa, Ya Ci Gyaransa

  • Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar mazabar Ajingi/Albasu/Gaya ya caccaki mataimakin kakakin Majalisar, Benjamin Kalu
  • Hon. Ghali Mustapha ya nuna damuwa kan yadda Kalu ke yawan kiran sababbin mambobin masu koyon aiki a kowane lokaci
  • Ghali ya bukace shi da ya rinka gyara maganganunsa inda ya ce duka mambobin Majalisar koyon aiki suke yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan Majalisar Tarayya daga Kano, Dakta Ghali Mustapha ya caccaki mataimakin kakakin Majalisa.

Hon. Ghali ya nuna bacin ransa kan yadda Benjamin Kalu ke yawan cin mutuncin sababbin mambobin Majalisar a kalamansa.

Dan Majalisar Tarayya daga Kano ya soki mataimakin kakakin Majalisar a Abuja
Hon. Ghali Mustapha daga Kano ya caccaki mataimakin kakakin Majalisar Tarayya kan nuna wariya. Hoto: Hon. Dr. Ghali Mustapha Tajjani.
Asali: Facebook

Kano: Hon. Ghali ya caccaki Benjamin Kalu

Ɗan Majalisar ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da @northern_blog ta wallafa da ya karade shafukan sadarwa.

Kara karanta wannan

El Rufai vs Uba Sani: Majalisar Kaduna ta bankado shirin mukarraban tsohon gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bai kamata Kalu ya rinka kiran sababbin mambobin ƴan koyo ba tun da dukansu koyo suke har da tsofaffin ƴan Majalisar.

Ghali da ke wakiltar mazabar Ajingi/Albasu/Gaya ya ce akwai yiwuwar sababbin mambobin sufi tsofaffin kwarewa a Majalisar duk da dadewarsu.

Hon. Ghali ya ci gyaran maganganun Kalu

"Ina son yi maka gyara kan maganganunka da kake yawan yi tsakanin sababbin mambobi da tsofaffi."
"Duk lokacin da kake rufe maganganunka kana yawan cewa sababbin mambobin koyon aiki suke, ya kamata ya rinka haɗawa da tsofaffin saboda kowa koyo yake yi."
"Na tabbata akwai sababbin mambobi da suka fi tsofaffin kwarewa duk da dadewarsu a Majalisar."

- Dakta Ghali Mustapha

A martaninsa, mataimakin kakakin Majalisar ya ce tabbas kowa koyo yake yi amma akwai wadanda suka fi kwarewa kan wasu.

Kawu Sumaila ya bukaci kirkirar sabuwar jiha

Kara karanta wannan

Sanata ya bayyana abin da yasa Tinubu ya gagara shawo kan tsadar abinci

Kun ji cewa Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya gabatar da kudirin neman kirkirar sabuwar jiha daga Kano.

Sumaila ya gabatar da kudirin ne a ranar Laraba 10 ga watan Yulin 2024 da ke neman samar da jihar 'Tiga' daga Kano.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta gabatar da kudurori domin kirkirar sababbin jihohi a Najeriya a ƴan kwanakin nan a Majalisun Tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.