Ribas: Wani Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Nada Sababbin Hadimai Sama da 300

Ribas: Wani Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Nada Sababbin Hadimai Sama da 300

  • Shugaban ƙaramar hukumar Ikwerri na rikon kwarya, Darlington Orji ya naɗa sababbin mataimaka na musamman sama da 300
  • Kantoman ya yi wannan naɗe-naɗen ne tun a watan Yuni bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya rantsar da shugabannin riƙo
  • Sai dai labarin ya bayyana ne bayan kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa gwamnatin tarayya ta riƙa tura kason kudi kai tsaye ga asusun ƙananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Wani shugaban karamar hukuma a jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Najeriya ya nada mataimaka sama da 300.

Rahotanni sun nuna cewa Darlington Orji, kantoman da Gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa domin ya kula da harkokin ƙaramar hukumar Ikwerre ne ya yi naɗin.

Kara karanta wannan

NLC Vs Tinubu: Ministoci 2 sun bayyana Lokacin da za a warware batun ƙarin albashi

Gwamna Siminalayi Fubara.
Wani shugaban ƙaramar hukuma a Ribas ya nada hadimai sama da 300 Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Premium Times ta kawo, shugaban ƙaramar hukumar Ikwerre na rikon ƙwarya ya naɗa hadimai sama da 300 ne ranar 26 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi waɗannan naɗe-naɗe ne kwanaki ƙalilan bayan Gwamna Fubara ya rantsar da kantomomi 23 a jihar Ribas gabanin lokacin da za a yi zaɓe.

Wannan labarin naɗe-naɗen ya fito ne a daidai lokacin da kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin bayar da cikakken ƴanci ga kananan hukumomi a Najeriya.

Ana zargin kantoman ya naɗa hadimai 600

Jerin sunayen hadiman da shugaban riko na ƙaramar hukumar Ikwerre ya naɗa ya nuna sun kai mutum 311, amma wasu na ikirarin sun haura 600.

Wasu daga cikin mutanen an naɗa su ne a matsayin mataimaka na musamman yayin da wasu kuma aka naɗa su a matsayin manyan mataimaka na musamman ga ciyaman.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame gidan wani da ake zargi da alaƙa da ƴan bindiga

A ranar Alhamis da ta gabata, aka tattaro cewa shugaban ƙaramar hukumar Obio-Akpor a jihar Ribas, Chijioke Ihunwo ya naɗa hadimai 100, rahoton The Cable.

James Ibori ya soki hukuncin kotu

A wani rahoton kuma Tsohon gwamnan jihar Delta ta caccaki hukuncin Kotun Koli kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da kuma gwamnonin jihohi 36.

James Ibori ya ce kwata-kwata hukuncin bai yi ba kuma koma-baya ne ga kasar wanda ya saba dokokin kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262