Ganduje Ya Gamu da Babban Matsala a Kano, Sanata Ya Fice Daga Jam'iyyar APC

Ganduje Ya Gamu da Babban Matsala a Kano, Sanata Ya Fice Daga Jam'iyyar APC

  • Yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan sarautar Kano, jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta ranar Jumu'a
  • Sanata Masud Doguwa ya jagoranci ɗumbin magoya bayansa daga APC sun koma PDP, ya ce gwamnatin Tinubu ba ta da alƙibla
  • Ya ce tsare-tsaren da gwamnatin APC ta ɓullo da su ba su da wani amfani ga talakawa illa ƙara jefa al'umma cikin mawuyacin hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da cikas a mahaifarsa jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan APC a Kano, Sanata Mas'ud Doguwa ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Kara karanta wannan

NLC Vs Tinubu: Ministoci 2 sun bayyana Lokacin da za a warware batun ƙarin albashi

Masud Doguwa.
Mas'ud El-Jibreel Doguwa ya koma.PDP a Kano Hoto: Masud El-Jibreel Doguwa
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa hakan na ƙunshe a wata sanarwa da Masud ya rattaɓawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a ranar Jumu'a, 12 ga watan Yuli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masud ya caccaki gwamnatin Tinubu

Masud Doguwa ya koma jam'iyyar PDP ne bayan ya zargi gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da cewa ba ta da alƙibla.

Ya kuma zargi shugaban ƙasa da ɓullo da tsare-tsaren da suka jefa ƴan Najeriya cikim ƙuncin rayuwa da baƙin talauci.

Meyasa ya bar APC zuwa PDP?

A sanarwar da ya fitar yau Jumu'a, Doguwa ya ce ya ɗauki matakin barin APC tare da ɗumbin magoya bayansa saboda tsare-tsaren da suka jefa al'umma cikin talauci.

Ya ce duk da irin gogewarsa a fagen siyasa, ba kasafai ake jawo su cikin harkokin jam’iyyar don su bayar da gudunmawar kawo ci gaba a APC ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta dauki mataki kan tubabbun 'yan Boko Haram 8,940

A rahoton Daily Post, sanawan ta ce:

"A siyasa idan ka gaza jawo gogaggun ƴan siyasa a jiki ta hanyar ba su ayyuka kana kokarin lalata masu siyasa ne da kuma sa su fara tunanin neman mafita a wani wurin."

Sanata Masud ya soki tsare-tsaren APC

Sanatan ya kuma nuna rashin jin dadinsa da manufofin gwamnatin APC, wadanda yake ganin suna da illa ga talakawa.

"Bayan na yi nazari sosai, na gano cewa wasu tsare-tsaren da APC ta zo da su suna karewa ne kan mutane kuma ba su dace da akidar siyasarmu ba.
"Wadannan manufofin sun fi cutar da al'ummar ƙasar nan da jefa su cikin mawuyacin hali fiye da amfaninsu," in ji shi.

Kotu ta amince a kamo Ganduje

A wani rahoton babbar kotun jihar Kano ta yanke hukunci kan bukatar lauyan gwamnatin jihar na ba da umarnin cafko Abdullahi Ganduje, mai dakinsa da wasu mutum 6.

Lauyan masu kara, Adeola Adedipe, SAN, ya nemi kotun ta ba da umarnin cafko tsohon gwamnan ne saboda ya ki bayyana gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262