Kananan Hukumomi: Atiku Ya Mayar da Martani Kan Hukuncin Kotun Ƙolin Najeriya

Kananan Hukumomi: Atiku Ya Mayar da Martani Kan Hukuncin Kotun Ƙolin Najeriya

  • Alhaji Atiku Abubakar ya nuna farin ciki bisa hukuncin da kotun ƙolin Najeriya ta yanke na ƴantar da ƙananan hukumomi daga hannun gwamnoni 36
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ayyana hukuncin a matsayin wata babbar nasara ga ƴan Najeriya
  • Sai dai duk da haka Atiku ya nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ke katsa landan a harkokin tattara kudin shigar kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Atiku Abubakar ya yaba da hukuncin kotun ƙoli wadda ta tabbatar da ƴancin tura kuɗin shiga kai tsaye ga asusun kananan hukumomi a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga ƴan Najeriya kuma alama ce ta ƙasar ta fara dawowa kan hanya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni za su yi zama kafin ba kananan hukumomi yanci, za su tattauna abu 1

Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku ya yi maraba da hukunta kotun koli kan ƴancin kananan hukumomi a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Alhaji Atiku ya faɗi haka ne yayin da yake martani bayan hukuncin kotun ƙoli a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hukunci kotun ƙoli ta yanke?

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa kotun koli ta kafa tarihi a hukuncin da ta yanke wanda ya ƴantar da ƙananan hukumomi wajen tura kasafin kudin shiga.

Kotun ta ce daga yanzu, tana umurtar gwamnatin tarayya ta tura kuɗi kai tsaye zuwa asusun gwamnatocin ƙananan hukumomi waɗanda al'umma suka zaɓa.

Wannan matakin dai ya kawo ƙarshen tura kudin ƙananan hukumomi zuwa asusun jihohi wanda aka saba yi a baya.

Atiku ya mayar da martani

Da yake nuna goyon bayansa kan hukuncin, Atiku ya ce:

"Ina tare da hukuncin da Kotun Koli ta yanke na cewa tsarin mulkin Najeriya ya kasu zuwa mataki uku, kuma daga cikinsu kananan hukumomi ya kamata su zama cibiyoyin ci gaba.”

Kara karanta wannan

Ribas: Wani shugaban ƙaramar hukuma ya nada sababbin hadimai sama da 300

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira da a bai wa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu ta kowane ɓangare fiye da rabon kuɗin shiga daga tarayya.

"Ina ganin ba a iya kason kuɗi daga tarayya kaɗai ya kamata mu ƴantar da ƙananan hukumomi ba, har da batun tattara kuɗaɗen shiga, shi ma a ba su ƴanci," in ji shi.

Shehu Sani ya yi martani

A wani rahoton kuma kun ji cewa Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi martani bayan hukuncin kotu kan kananan hukumomi.

Sanatan ya ce kusan ana nan a gidan jiya tun da wasu daga ciyamomin sai sun nemi izinin yadda za su kashe kudaden idan aka tura musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262