Muhammadu Sanusi II Ya Faɗi Yadda Za Magance Matsalolin da Suka Addabi Najeriya

Muhammadu Sanusi II Ya Faɗi Yadda Za Magance Matsalolin da Suka Addabi Najeriya

  • Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ce duka ƙalubalen da suka addabi Najeriya za a iya shawo kansu idan aka jajirce
  • Sarkin Kano na 16 ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar gwamnatin Kano a fadarsa ranar Alhamis
  • Sanusi II ya ce masarautar Kano za ta ci gaba da yiwa gwamnatin Abba Kabir Yusuf addu'ar samun nasara a mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammad Sanusi II ya ce galibin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu gadarsu aka yi.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin jihar Kano da suka kai masa ziyara a fadarsa ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kano: Dalilai 3 da za su hana Aminu Ado Bayero ƙwace sarauta daga hannun Sanusi II

Sarki Muhammadu Sanusi II.
Muhammadu Sanusi II ya ce za a iya magance kalubalen da ke addabar ƴan Najeriya Hoto: Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Twitter

Sanusi II ya ce bai kamata Najeriya ta ci gaba da zama wuri ɗaya ba, ya kamata ta yi hoɓɓasa domin magance ƙalubalen da suka zame mata ƙarfen ƙafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, yana da ƙwarin guiwar za a iya kawo karshen dukan ƙalubalen idan aka jajirce, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hanyar da za a magance matsalolin Najeriya

"Ina da yaƙinin ƙalubalen da suka addabi ƙasar nan gadonsu muka yi, haka jihohi duk sun gaji matsaloli to amma ya kamata mu sani kuka ba shi ne maganin damuwar ba.
"Ba zai yiwu mu tsaya muna kokawa kan abubuwan da suka faru a baya ba tare da mun ɗauki matakin gyara ba. Na san cewa Kanawa za su tsaya tsayin daka su magance kalubalen nan.
"Abin da ya fi kyau shi ne ka jagoranci al'umma ta yadda za su iya tsayawa da kafafuwansu kuma kada su durkusa ma kowa."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya fadi abin da shugabannin Arewa ya kamata su mayar da hankali a kai

Sanusi II ya yabawa gwmanatin Kano

Da yake yabawa gwamnatin Kano kan tsare-tsaren ilimi, fansho da kuma biyan kudin gratuti, Sarkin ya ce koda yaushe kofarsa a bude take domin neman shawarwari da tuntubar juna.

Muhammadu Sanusi II ya kara da cewa masarautar Kano za ta ci gaba da yiwa gwamnatin jihar addu’ar samun nasara.

Gwamna Adeleke ya dakatar da hadiminsa

A wani rahoton Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya dakatar da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin jama'a, Emmanuel Adebisi ranar Laraba.

Ya umarci dakatar da hadimin nan take har sai an yi bincike karkashin jagorancin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Osun, Kazeem Akinleye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel