2027: Gwamna Ya Yi Magana Kan Rade Radin Daukarsa Mataimakin Atiku a Zabe

2027: Gwamna Ya Yi Magana Kan Rade Radin Daukarsa Mataimakin Atiku a Zabe

  • Yayin da ake jita-jita da kiran Atiku Abubakar ya dauki Gwamna Douye Diri mataimakinsa, gwamnan ya yi watsi da lamarin
  • Gwamna Diri ya ce kwata-kwata bai bukatar hakan inda ya bukaci al'umma da su yi watsi da kiran saboda an yi ne domin wata manufa
  • Wannan na zuwa ne bayan wata kungiya mai suna Diri Angels ta shawarci daukar Diri a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri ya yi martani kan jita-jitar daukarsa mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2027.

Diri ya yi fatali da bukatar da wata kungiya ta yi domin Atiku ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

"A koma salon mulkinsu Sardauna": An fadawa Tinubu hanyar magance matsalolin Najeriya

Gwamna ya yi fatali da jita-jitar cewa Atiku ya dauke shi mataimaki a zaben 2027
Gwamna Douye Diri na Bayelsa ya ce bai bukatar zama mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2027. Hoto: @Atiku, @bukolasaraki.
Asali: Twitter

Diri ya magantu kan zama mataimakin Atiku

Leadership ta tattaro cewa wata kungiya ce mai suna Diri Angles ta ba da shawarar daukar gwamnan a zaben 2027 da ke tafe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai gwamnan ya barranta kansa da wannan kira inda ya bukaci al'umma da su yi watsi da shawarar domin ba ya bukata.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin sakataren yada labaransa, Daniel Alabrah a jiya Laraba 3 ga watan Yulin 2024, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Atiku: Diri ya yi fatali da jita-jita

"Ban rudu da wannan kira da ake yi ba, siyasa ta na dogara da ubangiji ne ba wai wasu 'yan siyasa da kulle-kullesu ba."
"Bukatar wadanda suka yi hakan shi ne kawo matsala sai dai ba su yi nasara ba saboda ba ni bukatar hakan ko kadan."

- Douye Diri

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Shehu Sani ya magantu da jin an nemi a hana Gwamna Abba fita kasar waje

Atiku ya ziyarci Buhari a Daura

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.

An yi ta rade-radin cewa Atiku ya kai ziyarar domin shirye-shiryen zaben 2027 da ake tunkara domin kwace mulkin Bola Tinubu

Sai dai a bangarensa, Atiku ya ce babu wani shirin siyasa a ziyarar kawai ya kai gaisuwa ne ga Buhari bayan kammala bukukuwan sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel