Gwamna Ya Dakatar da Babban Hadiminsa, Ya Umarci Ya Bar Ofis Nan Take
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya dakatar da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin jama'a, Emmanuel Adebisi ranar Laraba
- Ya umarci dakatar da hadimin nan take har sai an yi bincike karkashin jagorancin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Osun, Kazeem Akinleye
- Adeleke ya kuma umurci Kwamishinan Sufuri da ya tsara gudanar da taron sulhu a tsakanin bangarori masu adawa da juna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osogbo, jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke ya dakatar da Emmanuel Adebisi, babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin kungiyoyin fararen hula.
Mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 3, ga watan Yuli, 2024.
Hadimi ya gamu da fushin gwamnan Osun
Gwamna Adeleke ya bayar da umarnin dakatar da hadimin nan take ba tare da ɓata lokaci lokaci ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai gwamnan bai bayyana asalin dalilin da ya jawo ya ɗauki matakin dakatarwa kan Mista Emmanuel Adebisi ba.
A ruwayar Daily Post, sanarwar ta ce:
"Gwamna Adeleke ya dakatar da Emmanuel Adebisi nan take har sai an gama binciken da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jiha, Kazeem Akinleye zai jagoranta."
Gwamna Adeleke ya gargaɗi ma'aikatan sufuri
Bayan haka gwamnan ya gargaɗi ma'aikatan sufuri a faɗin jihar Osun da su gujewa duk wani abu da zai kawo tada zaune tsaye.
Ya umurci Kwamishinan Sufuri na jihar Osun da ya shirya wani taron sasantawa domin sulhunta dukkan bangarorin harkar sufuri da ke faɗa da juna..
"Jami'ai da sauran mambobin ƙungiyar sufuri su guji kauda hankalin al'ummar jihar Osun daga ayyukan aherin da ake yi, gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau'in tayar da tazoma ba.
"Ba za mu bari a mayar da hannun agogo baya ba, gwamnati mai ci ba za ta raga wa kowa kan tada yamutsi ba. Duk wata matsala da ta taso a bangaren sufuri, ya kamata a shawo kanta cikin ruwan sanyi."
- Gwamna Ade,ola Adeleke.
Gwamna Alia ya sa dokar kulle
Kuna da labarin Gwamna Hyacinth Alia ya sanya dokar zaman gida a karamar hukumar Ukum da kewayenta biyo bayan zanga-zangar da ta ɓarke ranar Laraba.
Matasa sun ɓarke da zanga-zanga a Sankera, hedkwatar da ƙaramar hukumar Ukum ne sakamakon kisan mutane 11 a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng