Majalisar Dokokin Jihar Imo Ta Ɗauki Zafi, Ta Dakatar da Ƴan Majalisa 4 Daga Aiki
- Shugaban majalisar dokokin jihar Imo, Hon Chike Olemgbe, a ranar Talata ya dakatar da ƴan majalisa huɗu bisa zargin shirin tsige shi
- Ya ce majalisar ta ɗauki wannan matakin ne a zaman sirri kuma daga yanzun an kwace dukkan kwamitocin da ke hannun ƴan majalisar da aka dakatar
- Sai dai har kawo yanzu babu wani martani daga ƴan majalisar da matakin ya shafa duk da wasu daga ciki sun halarci zaman yau Talata, 2 ga watan Yuli
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Majalisar dokokin jihar Imo ta dakatar da ƴan majalisa huɗu bisa zargin suna yunƙurin tsige shugaban majallisar, Chike Olemgbe.
Kakakin majalisar Honorabul Olemgbe ne ya sanar da ɗaukar wannan matakin a zaman ranar Talata, 2 ga watan Yuli, 2024.
'Yan majalisar da aka dakatar a Imo
‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da mamba mai wakiltar mazaɓar Ahiazu-Mbaise, Samuel Otuibe da mai wakiltar mazaɓar Ezinihitte-Mbaise, Henry Agbasonu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran su ne mai wakiltar mazaɓar Okigwe, Chidiebere Ogbunikpa da takwaransa na mazaɓar Oru ta Yamma, Dominic Ezerioha.
Meyasa majalisa ta dakatar da su?
Shugaban majalisar ya ce an dauki matakin dakatar da su ne a zaman da mambobin majalisar suka yi cikin sirri ranar Talata.
Chike Olemgbe ya ƙara da cewa majalisar ta kuma kwace dukkan kwamitocin da ke hannun mambobin da aka dakatar.
Majalisar Imo ta yi garambawul
Rahotanni sun bayyana cewa kakakin majalisar ya yi wasu ƴan gyare-gyare a kwamitoci a lokacin wannan zama da aka dakatar da ƴan majalisa huɗu.
Wasu daga cikin mambobin majalisar da aka dakatar waɗanda suka halarci zaman ranar Talata ba su yarda sun yi magana da ƴan jarida ba, cewar rahoton The New Telegraph.
Gwamnatin ta musanta ikirarin NLC
A wani rahoton kun ji Gwamnatin jihar Imo ta musanta ikirarin NLC ta ƙasa cewa har yanzun ba a fara biyan N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a jihar ba.
Kwamishinan yaɗa labaru, Declan Emelumba ya ce tun 2020 gwamna Uzodinma ya fara biyan N30,000, bayan cire tallafin mai ya ƙara zuwa N40,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng