Tsohon Jigon APC Ya Bayyana Illolin da Buhari Ya Yiwa Arewa, Ya Tabo Tinubu

Tsohon Jigon APC Ya Bayyana Illolin da Buhari Ya Yiwa Arewa, Ya Tabo Tinubu

  • Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a yankin Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Lukman Salihu ya ce tsohon shugaban kasar bai tsinana komai ga yankin Arewacin Najeriya ba a shekaru takwas da ya yi a kan mulki
  • Har ila yau, ya kuma bayyana irin yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ke kokarin tafarkin Buhari wajen yiwa Arewa illa a mulkinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a yankin Arewa maso yamma, Lukman Salihu ya bayyana kurakuran da Muhammadu Buhari ya yi a baya.

Lukman Salihu ya ce Buhari bai amfani Arewa da komai ba sai jawo mata tarin matsaloli da yayi cikin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Tsohon jigon APC ya wanke Tinubu kan halin da Arewa ke ciki, ya fadi mai laifi

Buhari da Tinubu
Tsohon jigon APC ya caccaki gwamnatin Buhari. Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Lukman Salihu ya bayyana abin da Bola Tinubu ke amfani da shi wajen cutar yan Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalolin da Buhari ya samar a Arewa

Lukman Salihu ya bayyana cewa mukin Buhari na shekaru takwas ya haifar da matsalolin da dama a yankin Arewa.

Dan siyasar ya ce Buhari ya samar da matsalolin tsaro, shaye-shaye, rashin aikin yi da talauci a Arewacin Najeriya, rahoton the Guardian.

Saboda haka Lukman ya ce babu wani amfani da Arewa ta samu a mukin da Muhammadu Buhari ya yi daga 2015 zuwa 2023.

Lukman: 'Ba hadin kai a Arewa'

Salihu Lukman ya bayyana cewa duk da tarin matsalolin amma yan Arewa sun kasa cewa komai a mulkin Bola Tinubu.

Ya kuma kara da cewa rashin hadin kai tsakanin shugabannin Arewa ne yasa gwamnatin Tinubu ba ta dauki wani mataki domin kawo karshen matsalolin ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya kinkimo wani gagarumin aiki da zai jagoranta a Arewa

Lukman Salihu ya gargadi Tinubu

A karkashin haka, Lukman Salihu ya yi kira da cewa gwamnatin Tinubu ta kiyayi abin da zai jawo fushin talakawa musamman a Arewa.

Ya ce yadda yunwa ta galabaita talakawa idan suka fara bori abin ba zai yi kyau ba ga ƙasa baki daya.

Ina kudin da Buhari ya kwato?

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kwamitin bincike na musamman kan kwato kadarorin gwamnati, Okoi Obono-Obla, ya yi magana kan yaki da rashawa.

Obono-Obla yi yi ikirarin cewa an mayar da dukiyar da kwamitin sa ya kwato a lokacin tsohon gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng