Kogi: Sanata Ta Tausaya Wa Mutanen Mazaɓarta, Ta Naɗa Sababbin Hadimai 100
- A kokarin ragewa al'umma radaɗin tsadar rayuwar da ake ciki, Sanata Natasha Akpoti ta naɗa sababbin hadimai 100 daga mazaɓar Kogi ta Tsakiya
- A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta ya fitar yau Jumu'a, Sanata Natasha ta ce za ta rika biyansu albashi duk wata har karshen wa'adinta a majalisa
- A cewarta, ta ɗauki wannan matakin ne domin inganta ayyukanta da kuma samun nasara a wakilcin da al'umma suka tura ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) a ranar Juma'a, ta sanar da nadin mataimaka 100 daga mazaɓarta.
Natasha ta ce matakin na daga cikin kokarinta na rage radadin talauci da kyautata rayuwa ga al’ummar mazabar ta watau Kogi ta Tsakiya.
Sanatar ta bayyan haka ne a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Arogbonlo Israel ya fitar ranar Jumu'a, 28 ga watan Yuni, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ƙara da cewa ta naɗa ƙarin hadimai 100 ne domin tabbatar da cewa ba ta ba al'ummar mazaɓarta kunya ba a majalisar dattawan Najeriya.
Sanata Natasha ta yi bayanin cewa an zabo sababbin hadiman ne daga gundumomi 57 da ke yankin mazaɓar Kogi ta Tsakiya domin inganta wakilcin da aka tura ta.
Meyasa Sanata Natasha ta naɗa hadimai 100?
A cewarta, duka hadiman da ta naɗa za su ci gaba da karɓan albashi duk wata na tsawon lokacin da za ta ɗauka a majalisa.
A rahoton Tribune Nigeria, Natasha ta ce:
"A matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, na ga ya dace na ɗauko mutane 100 masu hazaƙa daga dukkan gundumomi 57 na wannan mazaɓa domin inganta wakilcin da kuka tura ni."
"Za su rika karbar albashi duk wata na tsawon zamana a matsayin mamba a majalisar dattawa, inda za a fara biyan albashi na farko a ranar 30 ga Yuni, 2024.”
Natasha ta bayyana cewa waɗanda ta naɗa hadiman sun kunshi matasa, mata da dattijai kuma sun kasance mutane masu hazaka da basira, wasu kuma ƴan kasuwa ne.
NNPP ta yi magana kan tsige sarakunan Kano
A wani rahoton jam'iyyar NNPP ta yi ikirarin cewa sarakunan da tsohon gwamnan Kano Ganduje y naɗa ba su da banbanci da kwamishinoni.
Shugaban NNPP na Kano ya ce Ganduje ya naɗa Aminu Aso Bayero da sarakuna huɗu ne domin su taimake shi ya kawo Kano a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng