"Kowa Ya Yi Abin da Zai Iya": Kungiyar Gwamnoni Ta Fitar da Matsaya Kan Karin Albashi

"Kowa Ya Yi Abin da Zai Iya": Kungiyar Gwamnoni Ta Fitar da Matsaya Kan Karin Albashi

  • Kungiyar gwamna Kudancin Najeriya ta fitar da matsaya kan mafi karancin albashi da kungiyar kwadago ke nema
  • Kungiyar ta ce ya kamata a duba halin da jihohin ke ciki sannan a ba kowace jiha damar tattaunawa da kungiyar NLC a yankinta
  • Gwamnonin sun kuma bukaci sake tattaunawa da kungiyoyin kwadago na jihohi domin kowace jiha ta fitar da matsaya kan abin da za ta iya biya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Kungiyar gwamnonin Kudancin Najeriya ta yi zama na musamman kan mafi karancin albashi da ake tababa a kai.

Kungiyar ta bukaci ba kowace jiha damar biyan mafi karancin albashin abin da za ta iya duba da halin da ake ciki a jihohin da ma kasar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun yi taron gaggawa a Abuja, an bayyana abubuwan da aka tattauna

Kungiyar gwamnoni ta fitar da matsaya kan mafi karancin albashi
Gwamnonin Kudu sun bukaci ba kowace jiha damar biyan mafi karancin albashin da za su iya biya. Hoto: Dapo Abiodun.
Asali: Facebook

Albashi: Gwamnoni sun fitar da matsaya

Hakan ya biyo bayan matakin kungiyar kan mafi karancin albashi a ganawar da ta yi yi a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce duba da halin da ake ciki, kamata ya yi kowane gwamna ya tattauna da kungiyar NLC reshen jiharsa domin samun mafita

Gwamnonin sun kuma bukaci a ba su damar kula da albarkatun kasa da suke da shi a jihohinsu ba tare da katsalandan ba, Punch ta tattaro.

Gwamnoni sun bukaci iko a jihohinsu

Suka ce ba da lasisin masu hakar ma'adinai ba tare da sanya gwamnonin ciki ba shi ke kara rashin tsaro a jihohi da dama wurin neman ma'adinai.

Wannan mataki na gwamnonin na zuwa ne yayin da mataimakin shugaban kasa ya shiga wata ganawa da gwamanonin Najeriya

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta dauki mataki bayan Tinubu ya yi biris da maganar ƙarin albashi

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar kwadago ta NLC ya shiga yajin aiki a kwanakin baya kan mafi karancin albashi.

Kashim ya shiga ganawa da gwamnoni

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya shiga wata ganawa ta musamman da gwamnonin Najeriya a birnin Abuja.

Ganawar ba ta rasa nasaba da maganar mafi karancin albashi da ake tababa a kai cikin ƴan kwanakin nan da muke ciki bayan shiga yajin aiki.

Wannan taro na majalisar tattalin arziki na zuwa ne kwanaki kadan bayan Majalisar zartaswa ta ɗage tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel