"Bai Kyamar 'Yan Arewa," Kashim Shettima ya Kare Tinubu, Ya Yabawa Abba Gida Gida

"Bai Kyamar 'Yan Arewa," Kashim Shettima ya Kare Tinubu, Ya Yabawa Abba Gida Gida

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kare mai gidansa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ka zargin nuna wariya ga 'yan Arewa
  • Ya bayyana haka ne a Kano bayan karbar ta'aziyyar surukarsa, inda ya ce makiya ne ke kokarin darsa wani abu a zuciyoyin jama'a
  • Mataimakin shugaban ya kuma yaba da yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tarbe su ba tare da nuna bambanci irin na siyasa ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kare sukar da wasu ke yi ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na cewa ya tsani 'yan Arewa.

Mataimakin shugaban ya bayyana cewa masu kokarin shuka kiyayya ne ke yada labaran cewa shugaba Tinubu ya na nuna bangaranci ga 'yan Arewa

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi bayani kan sayowa shugaban kasa da mataimakinsa sabon jirgin sama

Bola Ahmed Tinubu
Mataimakin shugaban kasa ya musanta cewa shugaba Tinubu makiyin Arewa ne Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro cewa cewa Sanata Kashim Shettima ya bayyana haka ne a Kano lokacin da ya karbi tawagar gwamnatin tarayya a kan rasuwar surukarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu masoyin Arewa ne," Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu masoyin Arewa, musamman duba da mukaman da ya rabawa 'yan yankin.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa ministocin tsaro biyu daga yankin, sai shugaban, sai hafsan tsaro shi ma dan Arewa ne.

"Idan lokaci ya yi, za mu fitar da bayanan zai karyata labarin cewa shugaban kasa makiyin Arewa ne."

- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Kashim Shettima ya yabi Abba

Sannan rahoton ya ce Shettima ya yaba da yadda gwamnatin Kano ta nuna dattako duk da bambancin ra'ayi na siyasa.

Yayin da APC ta ke rike da Najeriya, jam'iyyar adawa ta NNPP ce ke mulki a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

Tinubu ya fadi abin da ya ruguza Arewa

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fadi abin da ya kara dagula rashin tsaro a Arewacin kasar nan.

Shugaban, wanda ya fadi haka a taron tsaro na kwanaki biyu da ya gudana a jihar Katsina ya ce rashin adalci shugabanni ne ya jawo rashin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel