Yahaya Bello: An Bayyana Wurin da Tsohon Gwamna Ya Ɓoye Domin Gudun Kamen EFCC

Yahaya Bello: An Bayyana Wurin da Tsohon Gwamna Ya Ɓoye Domin Gudun Kamen EFCC

  • Jigon PDP ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamna Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin jihar Kogi yana samun kariya daga Ahmed Ododo
  • Austin Okai, tsohon ɗan takarar majalisar tarayya ya faɗi haka ne yayin da EFCC ke ci gaba da koƙarin gurfanar da tsohon gwamnan a kotu
  • A watan Afrilu, 2024 hukumar EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo, inda ta roki al'umma su taimaka da bayanan wurin da ya ɓuya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Wani babban jigon jam'iyyar PDP, Austin Okai, ya fallasa wurin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ɓuya don kaucewa kamen EFCC.

Mista Okai ya bayyana cewa yanzu haka Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin Kogi da ke Lokoja ya ɓuya.

Kara karanta wannan

EFCC na tsaka da neman Yahaya Bello, gwamnan Kogi ya aikawa uban gidansa wasiƙa

Yahaya Bello.
Jigon PDP ya ce Yahaya Bello na ɓoye a wani wuri a gidan gwamnatin jihar Kogi Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

EFCC na neman kama Yahaya Bello

Tribune Nigeria ta tattaro cewa a watan Afrilun da ya gabata hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan layar zana da tsohon gwamnan ya yi domin kaucewa gurfanar da shi a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

EFCC ta buƙaci duk wanda ke da masaniyar wurin da Bello ya ɓuya, ya gaggauta kai rahoto ga ofishin hukumar ko kuma caji ofis mafi kusa.

Hukumar EFCC na zargin Yahaya Bello da halasta kuɗin haram da suka kai N80bn a lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar Kogi, rahoton Daily Post.

Ina Yahaya Bello ya samu mafaka?

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, jigon PDP ya yi zargin cewa Gwamna Ododo ya taka rawa har Bello ya gujewa EFCC ta hanyar dauke shi daga gidansa na Abuja.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya yi magana kan binciken da ake yi masa, ya fadi makomar Uba Sani a Kaduna

Autin Okai, tsohon ɗan takarar kujerar majalisar tarayya a inuwar PDP ya ƙara da cewa:

"Ana kyautata zaton Yahaya Bello yana boye a gidan gwamnatin jihar Kogi, inda gwamnan ke ba shi kariya.
"Maganar gaskiya ita ce, ana zargin Yahaya Bello ne ke bai wa Gwamna Ahmed Usman Ododo umarni daga wani boyayyen wuri a gidan gwamnatin."

Kano: Falana ya soki hukuncin kotu

A wani rahoton kuma Femi Falana ya soki hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a shari'ar sarautar Kano, ya ce akwai ruɗani.

Fitaccen lauyan mai rajin kare haƙƙin ɗan adam ya ce hukuncin yana da ɗaure kai domin kotun koli ta hana kotunan tarayya tsoma baki a sha'anin sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262