Ana Daf da Zabe, PDP Ta Sallami Tsohon Mataimakin Gwamna da Jiga Jiganta 2
- Jam'iyyar PDP a jihar Edo ta kori tsohon mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu kan zargin cin dunduniyarta
- Jam'iyyar ta dauki wannan matakin ne bayan ganawar kwamitin gudanarwa na PDP ana daf da gudanar da zabe
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Satumbar 2024 mai kamawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Ana daf da zaben gwamnan jihar Edo, jam'iyyar PDP ta kori tsohon mataiimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.
Jam'iyyar ta dauki matakin ne bayan zargin Shaibu da cin dunduniyarta ana saura watanni uku a yi zaben gwamnan jihar.
Edo: PDP ta sallami Philip Shaibu
Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya kuma sallami mataimakin shugaban jam'iyyar ta kasa a yankin Kudu maso Kudu, Dan Orbih a cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar a jihar, Ogie Vasco ya fitar a yau Laraba 19 ga watan Yuni.
Vasco ya ce jam'iyyar ta dauki wannan matakin ne bayan tuntubar duka masu ruwa da tsaki inda ya ce korar za ta fara aiki ne nan take, TheCable ta tattaro.
An tsige Philip Shaibu daga mukaminsa
Wannan na zuwa ne bayan Majalisar jihar Edo ta tsige Shaibu a matsayin mataimakin gwamnan jihar a watan Afrilun 2024.
Tsigewar na zuwa ne bayan kafa kwamiti mai mambobi bakwai domin kaddamar da binciken kan zarge-zarge da ake yi masa.
Daga cikin zarge-zargen akwai ba da shaidar karya da bankada bayanan sirri na gwamnatin jihar ba bisa ka'ida ba.
PDP ta sallami tsohon 'dan Majalisar Tarayya
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP a jihar Edo ta sallami tsohon mamban Majalisar Tarayya, Omorgie Ihama kan wasu zarge-zarge.
Jam'iyyar ta dauki wannan matakin ne ana daf da gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Satumbar 2024 wanda zamu shiga.
Kakakin jam'iyyar a jihar, Ogie Vasco shi ya tabbatar da haka inda ya ce ana zargin Ihama da cin dunduniyarta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng