Ganduje Ya Ƙara Rusa Ƴan Adawa, Manyan Jiga Jigai da Dubban Mutane 4450 Sun Koma APC

Ganduje Ya Ƙara Rusa Ƴan Adawa, Manyan Jiga Jigai da Dubban Mutane 4450 Sun Koma APC

  • Mambobin babbar jam'iyyar adawa PDP sama da 4,000 sun tattara kayansu sun koma jam'iyyar APC mai mulki a jihar Benuwai
  • Gwamna Hyacinth Alia ne ya karɓe su da kansa a wani taro da aka shirya lokacin da yake zagayen godiya ga al'ummar jihar da suka zaɓe shi
  • A jawabin da ya yi, ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da tsaro a faɗin jihar domin mutane su ci gaba da harkkinsu babu fargaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Yayin da manyan jam'iyyu ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027, jam'iyyar APC mai mulki ta samu ƙaruwa a jihar Benuwai.

Dubban mambobin jam'iyyar PDP waɗanda suka kai kimanin 4,450 sun watsar da tafiyar laima, sun koma jam'iyyar APC ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kano: NNPP tayi martani, ta ce APC na yunƙurin ƙwace mulki daga Gwamna Abba

Gwamna Alia na jihar Benuwai.
Gwamnan Benuwai ya karbi dubannin mambobin PDP da suka sauya sheka zuwa APC Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Mutane 4400 sun shigo jam'iyyar APC

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, dubban masu sauya sheƙar sun fito ne daga kananan hukumomi biyar da suka haɗa da Katsina-Ala, Ukum, Logo, Kwande da Ushongo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ne ya karɓi masu sauya shekar a wani taro da aka shirya yayin da yake zagayen godiya ga jama'a da suka zaɓe shi a 2023.

Gwamna Alia ya godewa mutanen Benue

Da yake jawabi a taron maraba da masu sauya sheƙar, Gwamna Alia ya miƙa godiya ga mutanen jihar bisa yadda suka amince suka zaɓe shi duk da cewa shi sabo ne a siyasa.

Alia ya kuma kara jaddada kudirinsa na mayar da ƴan gudun hijirar da hare-haren ƴan bindiga ya raba da mahallansu zuwa garuruwansu.

Haka nan kuma gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda ƴan bindiga suka addabi yankin Sankera, cibiyar noman doya a jihar da ke Arewa ta Tsskiya.

Kara karanta wannan

An shirin zaben gwamna, jigon PDP ya yi maƙarƙashiya, jam'iyya ta kore shi

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankala a faɗin jihar.

Sai dai ya ja hankalin jama'a cewa aikin samar da tsaro ba na gwamnati ba ne ita kaɗai, ya zama tilas kowa ya bayar da gudummuwa daidai gwargwado, rahoton The Nation.

Rikicin Kano: NNPP ta caccaki APC

A wani rahoton kuma Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta zargi APC da yunƙurin kwace mulki ta kowane hali a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.

A wata sanarwa da kakakin NNPP na ƙasa ya fitar, jam'iyyar ta tona yadda APC ke amfani da shari'a da jami'an tsaro don tayar da zaune tsaye a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262