An Miƙa Wa Bola Tinubu Sunan Wanda Ya Kamata Ya Naɗa a Matsayin Ministan Jin Ƙai

An Miƙa Wa Bola Tinubu Sunan Wanda Ya Kamata Ya Naɗa a Matsayin Ministan Jin Ƙai

  • Naƙasassu a jam'iyyar APC ta Kudu maso Yamma sun miƙa wa Bola Tinubu sunan wanda ya kamata ya naɗa a matsayin ministan jin ƙai
  • Sun bukaci shugaban ƙasa ya naɗa sabon ministan jin ƙai ne yayin da suka kai masa ziyarar Barka da Sallah a jihar Legas
  • Haka nan sun yi kira ga ƴan Najeriya su jure wahalar da aka shiga kuma su marawa gwamnatin Tinubu baya domin saita Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos- Masu buƙata ta nusamman a jam’iyyar APC ta shiyyar Kudu maso Yamma, sun yi kira ga Bola Tinubu ya nada sabon ministan jin kai.

Naƙasassun sun miƙa wannan bukata ne a lokacin da suka kai ziyarar Barka da Sallah ga Shugaban Ƙasa Tinubu a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara tsanani, APC ta buƙaci Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jiha 1

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Masu buƙata ta musamman sun kai wa Tinubu ziyarar barka da Sallah a Legas Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Minista: An nemi Tinubu ya naɗa Tejuoso

Masu nakasar sun ba shugaban ƙasar shawarin ya ɗauko Dokta Adenike Tejuoso ya naɗa shi a matsayin sabon ministan harkokin jin kai da yaye talatauci, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar nakasassun APC na shiyyar, Abayomi Soetan, ya ce Tejuoso ya fi kusanci da mutanen da ke da bukatu na musamman da sauran rukunin mabuƙata.

Ya bayyana Tejuoso a matsayin abin koyi da ya ba da gudunmawa mai tarin ya wajen ci gaban al’umma da kasa baki ɗaya, rahoton Vanguard.

Soetan ya kara da cewa Tejuoso ya tallafawa marasa galihu a lokuta da dama, bisa haka suke ganin shi ya fi cancanta da kujerar ministan jin ƙai.

Naƙasassu sun tura saƙo ga ƴan Najeriya

Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da su marawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu baya duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki wanda ya kawo tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

"So kake yi Tinubu ya mutu": Fadar shugaban kasa ta caccaki Peter Obi

Mista Soetan ya roƙi ƴan Najeriya kar su gaji kuma su ci gaba da nuna juriya, inda ya ƙara da cewa duka wannan wahalhalun da ake ciki za su zama tarihi nan gaba.

Idan ba ku manta ba shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin kai da yaye talauci, Dokta Betta Edu, bisa zarginta da hannu a badaƙalar wasu kuɗi.

Jam'iyyar APC ta yi kira ga Tinibu

A wani rahoton kun ji cewa APC ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci domin kawo karshen kashe-kashen rayuka a jihar Ribas.

Shugaban APC na rikon kwarya a jihar, Tony Okocha ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan Gwamna Simi Fubara ya rantsar da sababbin ciyamomi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel