Gwamna Ya Fadi Yadda APC Za Ta Kwato Mulki a Jihar Edo Domin Samun Karin Jihohi Kudu

Gwamna Ya Fadi Yadda APC Za Ta Kwato Mulki a Jihar Edo Domin Samun Karin Jihohi Kudu

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana aniyarta na samun karin gwamnonin jihohi a kudancin Najeriya nan gaba kadan
  • Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a birnin Kalaba
  • Legit ta tattauna da wata 'yar asalin jihar Edo, Enefele Nkem Blessing domin jin ra'ayinta a kan yadda zaben jihar zai gudana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Cross River - Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ya ce APC ta daura damarar kwace wasu jihohin kudu maso kudu daga hannun jam'iyyun adawa.

Gwamnan ya fadi haka ne yayin da ake shirin fara zaben gwamna a jihar Edo a watanni ƙaɗan masu zuwa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ƙara rusa ƴan adawa, manyan jiga-jigai da dubban mutane 4450 sun koma APC

Zaben Edo
Jam’iyyar APC ta bukaci karin jihohi a Kudu ana shirin zaben Edo. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamna Bassey Otu ya fadi haka ne yayin wani taron da jam'iyyar APC ta shirya a birnin Kalaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC za ta kwato jihohin kudu

A yayin taron jam'iyyar APC da ya gabata a Kalaba, gwamna Bassey Otu wanda shi ne jagoran APC a shiyyar kudu maso kudu ya ce jam'iyyar za ta kara kama jihohi a yankin.

Gwamna Bassey ya ce yana da karfin gwiwa a kan cewa za su kara samun nasara a jihohin kudu musamman a jihar Edo da ake kokarin yin zaɓe.

Meyasa APC ke neman karin jihohi?

Bassey Otu ya ce shi kadai ne gwamnan a jam'iyyar APC a yankin kudu maso kudu kuma ya gaji da zaman kaɗaici saboda haka za su yi kokarin samun karin jihohi, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Bayan haka shugaban kasa Bola Tinubu ma ya bayyana cewa akwai buƙatar samun karin jihohi a yankin domin samun albarkar da APC ke samarwa a ƙasa.

APC na neman nasara a zaben Edo

A watan Satumba mai zuwa ne za a yi zaben gwamna a jihar Edo kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa za ta yi dabarun da ta yi wajen samun nasara a jihar Imo domin kwace mulki a jihar Edo.

Gwamna Bassey Otu ya ce yana da tabbas kan cewa jihar Edo ba za ta kuɓuce musu ba saboda sun yi tanadi mai kyau domin tunkarar zaben.

Legit ta tattauna da Enefele Blessing

Wata 'yar asalin jihar Edo, Enefele Nkem Blessing ta zantawa Legit cewa yanzu kan mage ya waye yan siyasa ba za su rudi mutane da dadin baki ba.

Blessing ta ce mutane suna duba dan takaran da zai iya cire musu kitse a wuta ne ba jam'iyya ba saboda haka duk wanda suka fitar da dan takara nagari ne ke da alamar nasara a zaben.

Kara karanta wannan

An shirin zaben gwamna, jigon PDP ya yi maƙarƙashiya, jam'iyya ta kore shi

Gwamna Bassey Otu zai kara albashi

A wani rahoton, kun ji cewa a lokacin da aka yi bikin ranar ma'aikata a Najeriya, gwamnan jihar Kuros Riba ya amince da sabon mafi karancin albashi.

Gwamna Bassey Otu ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan jihar inda ya ce sun yi karin ne duba da halin da jihar ke ciki na kuncin rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel