Masarautun Kano: Sanusi II Ya Fadi Musabbabin Cire Shi da Ganduje Ya Yi Daga Sarauta

Masarautun Kano: Sanusi II Ya Fadi Musabbabin Cire Shi da Ganduje Ya Yi Daga Sarauta

  • Muhammadi Sanusi II ya bayyana musabbabin cire shi daga kujerar sarautar Kano da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi
  • Sanusi ya ce kowa ya sani magana ce ta siyasa inda ya ce shiyasa bai kalubalanci matakin ba a wancan lokaci
  • Sarkin ya ce ko marar tunani ya ji dalilin da gwamnan ya fada a wancan lokaci ya san shirme ne kawai babu kamshin gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan musabbabin tsige shi daga sarautar Kano.

Sanusi II ya zargi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da tube kawai saboda siyasa.

Sanusi II ya zargi Ganduje da tube shi saboda siyasa
Muhammadu Sanusi II ya ce siyasa ce silar tube shi da Ganduje ya yi a Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: UGC

Kano: Sanusi II ya magantu kan sarauta

Kara karanta wannan

Kano: Ba kamar Aminu Ado ba, Sanusi II ya fadi abin da zai kai shi kotu kan sarauta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya bayyana haka ne a yau Asabar 15 ga watan Yuni yayin hira ta musamman da jaridar The Sun.

Ya ce Ganduje ya tube shi a sarautar Kano ne kawai saboda zargin wai ba yayin biyayya inda ya ce wannan ba dalili ba ne.

Sanusi II ya fadi dalilin kalubalantar hukuncin

"An tambayi gwamnan, mene dalilin rashin yin biyayyar? Ya ce wasu lokutan ana gayyata na ganawa amma ba ya zuwa."
"Duk ɗan Najeriya mai hankali idan ya ga wannan batu ba zai dauki me maganar da muhimmanci ba ace saboda rashin mutunta gayyata aka cire Sarki."
"Kowa ya san ba haka ba ne dalili, shiyasa na ce ba zan dauki mataki ba, na kalubalanci matakin ne saboda kokarin killace ni a cikin gida."

- Muhammadu Sanusi II

Sarkin ya ce bai kalubalanci matakin saboda cire shi a sarauta ba sai dai domin take hakkinsa inda ya ce kowa ya san siyasa ne dalilin tube shi a sarauta.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya tabo batun wani gwamna ya tsige shi a gaba, ya fadi matakin dauka

Sanusi II ya caccaki Ganduje kan masarautu

Kun ji cewa Muhammadu Sanusi II ya soki Abdullahi Ganduje kan kokarin lalata al'adun jihar Kano bayan ƙirƙirar masarautu.

Sarkin ya ce shekaru fiye da 1,000 masarautun Kano na nan amma babu wanda ya bukaci neman kara wasu a jihar.

Sanusi II ya ce Gwamna Abba Kabir ya yi kokari wurin gyara barnar da Ganduje ya yi lokacin da ya ke mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel