EFCC: An Samu Matsala a Shirin Gurfanar da Tsohon Gwamna Kan Badaƙalar N80bn
- Kotu ta sauya ranar gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello daga yau Alhamis 13 zuwa 27 ga watan Yunin 2024
- Hakan ya faru ne sakamakon buƙatar da lauyoyin EFCC suka nema na ɗage ranar saboda rashin isasshen lokacin zuwa kotu
- Lauyan Yahaya Bello, Adeola Adedipe, SAN ya ce ya yi mamakin yadda lauyan EFCC ya halarci zaman kotu yau Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar kotun tarayya ta sauya ranar da za a gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan tuhumar satar maƙudan kuɗi da suka kai N80bn.
Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ce ta zama silar sauya ranar daga 13 ga watan Yuni zuwa 27 ga watan Yunin 2024.
Kamar yadda The Nation ta kawo a rahoto, EFCC ta janye buƙatar ɗage ranar gurfanar da Yahaya Bello ba tare da ta sanar da lauyoyin tsohon gwamnan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta ɗage shari'ar Yahaya Bello
Sakamakon haka aka sake zaɓar ranar 27 ga watan Yuni domin kawo Yahaya Bello gaban kotun kan tuhume-tuhume halasta kuɗin haram wanda EFCC ta shigar.
An cimma wannan matsaya ne yayin zaman kotun na yau Alhamis, 13 ga watan Yuni, 2023.
Yahaya Bello: Lauyoyin EFCC sun kai kukansu
A zaman, ɗaya daga cikin lauyoyin Yahaya Bello, Adeola Adedipe, SAN, ya shaidawa kotu cewa lauyoyin EFCC sun same su sun ce ranar 13 ga Yuni ba tayi masu ba.
Ya ce lauyoyin hukumar yaƙi da rashawar sun faɗawa Aliyu AbdulWahab, SAN, ɗaya daga cikin lauyoyin wanda ake ƙara cewa suna son a canza ranar zaman kotu.
Sakamakon haka lauyoyin tsohon gwamnan Kogi suka amince a canja ranar zuwa lokacin da ya dace kuma masu ƙara ke da sarari, rahoton Leadership.
Ya ce ya yi mamaki da ya samu labarin cewa lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya halarci zaman kotu duk da rokon da suka yi na sauya ranar zaman.
Gwamna ya koma makaranta a Uyo
A rahoton nan kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom ya koma jami'ar Uyo (UNIUYO) domin ya ƙarasa karaun digirinsa na uku (PhD)
Fasto Umo Eno ya gabatar da babin farko a kundin aikin binciken da zai yi a gaban kwamitin malaman jami'ar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng