Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Faɗi Wasu Gwamnoni da Ke Amfani da Ƴan Daba Su Murde Zaɓe
- Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya zargi wasu gwamnonin jihohi da amfani da ƴan daba wajen maguɗin zaɓe don cimma burinsu na siyasa
- Tsohon shugaban ƙasar ya ce maimakon gwamnoni su gina matasan ta hanyar da gwamnati za ta amfana da su, sun zaɓi mayar da su ɓata gari
- Jonathan ya yaba da yadda Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ɗauki yaran da suka kammala digiri da daraja ta farko aiki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya yi zargin cewa wasu gwamnoni na amfani da ɓata gari wajen cimma burinsu na siyasa.
Jonathan ya ce gwamnonin sun mayar da hankali wajen shirya ɓata gari don maguɗin zaɓe, maimakon su taimaka masu su zama kwararru a aikin gwamnati.
Ya bayyana haka ne a Benin ranar Laraba a wurin kaddamar da sakatariyar jihar Edo da Gwamna Godwin Obaseki ya sabunta, Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban kasar ya ce lokacin da shugaban ma’aikatan Edo ya sanar cewa Obaseki ya dauki ɗaliban da suka gama digiri da shaida mafi daraja aiki, ya ji dadi matuka.
Jonathan ya soki wasu gwamnoni
"Mutum mai hangen nesa kamar Obaseki ne kaɗai zai iya haka. A taƙaice mun zo wani zamani da idan ka je wasu jihohin za ka ga gwamnoni suna shirya ɓata gari saboda siyasa.
"Suna ƙarafafawa ɓata gari guiwa domin su yi amfani da su wajen murde zaɓe, su sato akwatu, su ɗauki wukake da makamai su nufi mutane a wurin zaɓe.
"Amma a nan Edo kana ƙarfafa masu hazaƙa, mutane masu hazaka ba ƴan jam'iyya ɗaya ba ne, akwai su a kowace jam'iyya."
- Goodluck Jonathan.
Tun da farko, Gwamna Obaseki ya ce ya gyara sakatariya saboda yana da yaƙinin cewa dole sai tsare-tsaren gwamnati sun tafi daidai za a samu ci gaba a jihar, Gazette Nigeria ta rahoto.
Tinubu ya faɗi dalilin zamewa a Abuja
A wani rahoton Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a karon farko kan zamewar da ya yi ya faɗi a lokacin hawa motar fareti a birnin tarayya Abuja.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa shi ɗan yarbawa ne kuma ya ɗan taɓa wasan al'adar da ake kira dobale domin murnar ranar dimokuraɗiyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng