Jam'iyyar APC Ta Ɗauki Zafi, An Dakatar da Wasu Manyan Jiga Jigan Jam'iyya

Jam'iyyar APC Ta Ɗauki Zafi, An Dakatar da Wasu Manyan Jiga Jigan Jam'iyya

  • Ga dukkan alamu rigima na neman ɓarkewa a jam'iyyar APC reshen jihar Abia a lokacin da aka dakatar da wasu manyan jiga-jigai
  • Masu ruwa da tsakin APC a Aba ta Arewa sun yanke shawarar dakatar da wasu mambobi bisa zargin rashin ɗa'a, ladabi da kuma sojan gona
  • Wannan mataki dai ya tayar da ƙura a APC ta jihar kuma har yanzun babu wata sanarwa a hukumance daga uwar jam'iyya ta Abia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - All Progressives Congress (APC) reshen ƙaramar hukumar Aba ta Arewa a jihar Abia ta dakatar da wasu manyan ƙusoshin jam'iyyar.

Masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC a yankin sun tabbatar da ɗaukar matakin dakatarwa kan mambobin bisa zarge-zargen rashin ladabi da biyayya da kuma sojan gona.

Kara karanta wannan

Neja: Abubuwan sun rikice a APC, an dakatar da shugabar mata a Arewa

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.
APC da dakatar da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar a Abia Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC ta dakatar da 'ya 'yanta

Matakin na kunshe ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Yuni, 2024 wadda aka tura zuwa ga shugaban APC na jihar Abia, Kingsley Ononogbu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, masu ruwa da tsakin APC a Aba sun amince da dakatar da jiga-jigan ne a wani taro da suka gudanar.

Sanarwar dakatarwar da masu ruwa da tsaki suka sanya wa hannu, ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin mambobin APC tun bayan lokacin da ya bayyana a soshiyal midiya.

Hon. Tony Anuforo, shugaban APC a Aba ta Arewa ya rattaɓa hannu a takardar dakatar da mambobin.

Jiga-jigan da APC ta dakatar

Wadanda aka dakatar sun hada da Kwamared Uche Moses (Eziama Ward 1), Mista Uzoma Nwogu (Umuola Ward 8), da Mista Uhiara Humphrey (Ward 4) da dai sauransu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarna, sun tafi da matafiya da yawa a hanyar zuwa Abuja

Har zuwa lokacin da muke haɗa wannan rahoto, jam'iyyar APC ta jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan dakatar da waɗannan jiga-jigai.

Haka nan kuma a nasu ɓangaren, waɗanda matakin dakatarwar ta shafa ba su ce komai ba kan abin da ake tuhumar sun aikata, jaridar Vanguard ta kawo.

APC ta samu galaba a Yobe

A wani rahoton kuma jam'iyyar APC ta samu nasara yayin da aka sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 17 na jihar Yobe.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wacce ta sanar da sakamakon zaɓen ta ce jam'iyyar ta lashe dukkanin kujerun ƙananan hukumomin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel