'Yan Majalisa Sun Nemi a Mayar da Wa'adi 1 ga Shugaban Kasa, Sun Faɗi Adadin Shekaru

'Yan Majalisa Sun Nemi a Mayar da Wa'adi 1 ga Shugaban Kasa, Sun Faɗi Adadin Shekaru

  • Tawagar ƴan majalisar wakilai ta ƙasa na neman a sauya wa'adin shugaban ƙasa zuwa zango ɗaya tal na shekaru shida
  • Haka nan 'yan majalisar tarayya sun buƙaci a gyara kundin tsarin mulkin domin saka tsarin karɓa-karɓa tsakanin shiyyoyin kasar nan
  • Baya ga wannan, sun nemi a mataimakan shugaban ƙasa su zama biyu, sannan zaɓen gwamnoni ya koma rana guda

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wasu mambobin majalisar wakilan tarayya na neman a yiwa kudin tsarin mulkin Najeriya 1999 garambawul domin a saka tsarin karɓa-karɓa.

Tawagar ƴan majalisar sun bukaci hakan domin a tsara yadda shiyyoyi shida na Najeriya za su riƙa karɓa-karba a kujerar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Bayan canja taken ƙasa, Tinubu zai karɓi ƙudurin sauya tsarin mulkin Najeriya

Majalisar wakilan tarayya.
Yan majalisa na neman a mayar da wa'adi ɗaya na shekaru 6 ga shugaban ƙasa Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Wa'adin shekara 6 ga shugaban ƙasa, gwamnoni

A rahoton Punch, an ji sun nemi a yiwa kundin tsarin mulki gyara domin a mayar da wa’adi guda na shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnonin jihohin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisa mai wakiltar Ideato ta Kudu da Arewa daga jihar Imo, Ikenga Ugochinyere ne ya bayyana hakan madadin ƴan majalisar ranar Litinin a Abuja.

Yan majalisar sun nemi a ƙara mataimakan shugaban kasa su zama biyu, daya daga yankin Kudu, daya kuma daga yankin Arewacin kasar nan.

Sun kuma nemi a yiwa dokar zaɓe ta 2022 garambawul domim a riƙa gudanar da zaɓen gwamnonin jihohi a rana ɗaya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Atiku da Obi na son a koma wa'adi 1

Wannan ba shi ne kron farko da aka fara kiraye-kirayen sauya wa'adin shugaban ƙasa daga zango biyu na shekaru huɗu zuwa zango ɗaya na shekara shida ba.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Sokoto ta ceto mutum 250 daga hannun 'yan bindiga

Manyan ‘yan adawa irinsu Atiku Abubakar da Peter Obi sun yi kira da a mayar da ofishin shugaban kasa wa’adi daya bayan sun sha kaye a zaben 2023 a hannun Bola Tinubu.

NLC ta yi watsi da tayin N62,000

A wani rahoton kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi watsi a tayin N62,000 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin mafi karancin albashi.

Mataimakin babban sakataren kungiyar, Chris Onyeka ya bayyana cewa ko N100,000 ba su kawo za su amince da shi ba, ballantana N62,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel