"Abin da Ya Sa Bola Tinubu Ya Fi Atiku da Obi Cancantar Zama Shugaban Ƙasa a 2023"
- Doyin Okuoe ya bukaci ƴan Najeriya su bai wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu lokaci kafin su fara alƙalanci kan kamun ludayinta
- Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce babu ɗan takarar da ya fi Tinubu cancantar zama shugaban kasa a babban zaɓen 2023
- A cewarsa, Tinubu ya karɓi mulki ne a lokacin da ake ganin kamar Najeriya ta zauna babu shugabanci na shekara takwas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya bayyan shi a matsayin wanda ya fi kowa cancanta a zaben 2023.
Bola Tinubu ne ya samu nasara a zaben, inda Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour suka zo na biyu da na uku.
Okupe, wanda shi ne daraktan yakin neman zaben Peter Obi a farko, ya ce da ya yi nazari sai ya gane cewa Tinubu ne ya fi dacewa da wannan aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv, Mista Okupe ya ce:
"Bari in gaya muku, a cikin dukkan mutanen da suka tsaya takarar Shugaban kasa a 2023, Bola Tinubu ba tsaran sauran ba ne, shi ya fi cancanta.
“Na ga Peter Obi, ina tare da Atiku Abubakar, na kuma san Bola Tinubu shekaru da yawa da suka wuce."
"Duk da bana tare da shi tsawon shekara 7 zuwa 8 amma ina ganin shi ne ɗan takarar da ya ciri tuta, ya fi sauran gogewa, ilimi da himmar yin aiki.
Shugaba Tinubu na bukatar lokaci
Okupe ya bayyana cewa bai kamata ƴan Najeriya sun fara yankewa gwamnatin Tinubu hukunci ba kamar yadda suka saba yiwa gwamnatocin baya.
A cewarsa, ya kamata su tuna cewa Tinubu ya karɓi kasar nan nw a lokacin da ake tunanin kamar an shafe shekaru takwas ana yi wa ƙasar illa, The Nation ta ruwaito.
Da yake nanata cewa shekara daya ta yi kadan a hukunta gwamnati mai ci, Okupe ya ce idan ‘yan Najeriya za su ba Tinubu lokaci, zai ba su mamaki.
NLC za ta iya komwa yajin aiki
A wani rahoton kuma alamu na nuna abu ne mai wahala ƴan kwadago su amince da N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa ya ƙarƙare tattaunawa kuma ya faɗi adadin kuɗin da yake ganin za su inganta rayuwar ma'aikata.
Asali: Legit.ng