Minista Ya Fadi Dalilin Umartar Manyan Sakatarori Su Durkusawa Tinubu a Abuja

Minista Ya Fadi Dalilin Umartar Manyan Sakatarori Su Durkusawa Tinubu a Abuja

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya kare matakinsa na umartar sakatarorin din-din-din su durkusawa Bola Tinubu
  • Wike ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiya ga Tinubu bayan amincewa da mukamin sakatarorin a ma'aikatar FCTA
  • Wannan na zuwa ne bayan cece-kuce da aka ta yi kan durkusawa Tinubu da wasu manyan sakatarorin FCTA suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya magantu bayan ce-ce-ku-ce kan durkusawa da sakatarorin din-din-din suka yiwa Bola Tinubu.

Nyesom Wike ya ce shi ya ba su umarnin durkusawa saboda irin karamci da ya yi musu a ma'aikatar Abuja (FCTA).

Kara karanta wannan

Minista ya mika mafi karancin albashin N105,000 ga Tinubu? an fayyace gaskiya

Minista ya magantu kan durkusawa Tinubu Abuja
Nyesom Wike ya kare matakin umartan manyan sakatarori durkusawa Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wike ya kare kansa kan durkusawa Tinubu

Ministan ya bayyana haka ne bayan durkusawar ta jawo ka-ce-na-ce daga ƴan Najeriya wanda suke ganin hakan bai kamata ba cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Rivers ya ce Tinubu ya cancanci haka ganin yadda ya kirkiro sakatarorin ma'aikatar wanda babu su a baya.

Ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiya ga Tinubu bayan dawo da martabarsu a matsayin sakatarorin din-din-din a birnin, Daily Trust ta tattaro.

Wike ya fadi musabbabin durkusawa Tinubu

"Kwanaki biyu da suka wuce, mun yi kokarin yin godiya ga Tinubu bayan dawo da martabar wasu ma'aikata da suka cire rai a aiki wurin kai mataki mai girma."
"A baya a FCTA babu sakatarorin din-din-din, amma Tinubu ya ce dole za su girma a aiki har zuwa wannan mataki."

Kara karanta wannan

'Dan a mutun Tinubu ya gindaya sharudan raba gari da shi, ya fadi alaƙarsa da Atiku

"Shugaban kasa ya amince da hakan, ni kuma na kira sakatarorin da abin ya shafa domin nuna godiya ga Tinubu."
"Amma mutane da dama ba su iya ganin abu mai kyau sai dai kullum su yi ta kushewa."

- Nyesom Wike

Bola Tinubu ya yabawa Nyesom Wike

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mukamin da ya nada wanda bai yi nadama ba a gwamnatinsa.

Tinubu ya ce Ministan harkokin birnin Abuja, Nyesom Wike na daga mukami mafi kyau a cikin sauran mukaman da ya nada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.