Ana Daf da Zabe, Ɗan Takara a Jam'iyyar Kwankwaso Ya Janye Daga Neman Gwamna
- Ɗan takarar jam'iyyar NNPP a zaben jihar Ondo, Israel Ayeni ya yanke shawarar janye takara daga zaben watan Nuwambar
- Ayeni ya tabbatar da haka a yau Laraba 5 ga watan Yuni inda ya ce ya dauki matakin ne domin jam'iyyar NNPP
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a jihar a ranar 16 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Ɗan takarar gwamna a jam'iyyar NNPP a jihar Ondo ya janye daga kudirinsa na neman takara.
Mista Israel Ayeni ya tabbatar da janye takarar a yau Laraba 5 ga watan Yuni a birnin Akure da ke jihar.
NNPP: Ayeni ya lashe zaben fidda gwani
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya bayyanawa ƴan jaridu inda ya ce ya yi haka ne saboda ci gaban jam'iyyar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan takarar ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani da kuri'u 100 kan Farfesa Ibrahim Ajagunna da aka gudanar a ranar 26 ga watan Afrilu, TheCable ta tattaro.
"Ni Israel Ayeni, dan takarar jam'iyyar NNPP a zaben 16 ga watan Nuwamba a Ondo na janye takarar neman gwamna."
"Na yanke shawarar janye takarar ne domin kare muradun jami'iyyar NNPP."
- Israel Ayeni
APC ta dakatar da ƴar takarar gwamna
Har ila yau, jam'iyyar APC a gundumar Ode-Aye a karamar hukumar Okitipupa a jihar Ondo ta dakatar da Injiniya Folake Omogoroye.
Injiniya Folake Omogoroye ita ce ƴar takara mace da ta fafata a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar ranar 20 ga watan Afrilun 2024.
Kwankwaso ya magantu kan matsalolin Arewa
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya magantu kan tabarbarewar lamura da suka addabi yankin Arewacin Najeriya.
Kwankwaso ya bayyana rashin iya shugabanci da rashin adalci a matsayin manyan abubuwa da ke lalata lamura a yankin.
Tsohon gwamnan Kano ya koka kan yadda ake yaudarar mutane da atamfa da taliya domin zaben azzaluman shugabanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng