Duk da Umarnin Sammaci, Ganduje Ya Yi Biris, Ya Kaddamar da Muhimmin Aiki ga APC

Duk da Umarnin Sammaci, Ganduje Ya Yi Biris, Ya Kaddamar da Muhimmin Aiki ga APC

  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da rijistar mambobin jam'iyyar ta yanar gizo a Abuja
  • Ganduje ya bayyana cewa yin wannan rijista zai taimaka matuka ga ƴaƴan jam'iyyar wurin neman takara da kuma mukamai a gwamnati
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin rigimar tuge shi daga kujerarsa tare da zargin badakala yayin da yake gwamna a Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Dakta Abdullahi Ganduje ya kaddamar da fara rijistar mambobin jam'iyyar ta yanar gizo.

Ganduje ya kaddamar da shirin ne a yau Laraba 5 ga watan Yulin a Abuja inda ya bayyana ka'idojin yin rijistar.

Kara karanta wannan

APC ta yi hannun riga da wani tsohon gwamna, ta cire shi daga jagororin jam'iyya

Ganduje ya kaddamar rijistar mambobin APC a Abuja
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya kaddamar da rijistar mambobinta a Abuja. Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: Twitter

Ganduje ya bayyana amfanin rijistar APC

Shugaban APC ya ce za a bukaci lambar katin ɗan kasa wato NIN kafin yiwa wani 'dan jam'iyya rijista ta yanar gizo, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk wanda zai yi rijista a matsayin ɗan jami'yyar APC sai ya kawo bayanansa wanda ya yi dai-dai da na lambar NIN."
"Hakan zai bamu damar sanin bayanan mutum da kuma yawan mambobin da muka yiwa rijista a jami'yyar."
"Sannan rijistar za ta taimaka wurin neman mukami ko takarar siyasa ga duka mambobinmu da kuma amfani wurin ɗaukar matakai."

- Abdullahi Ganduje

Kotu ta umarci tura sammaci ga Ganduje

Wannan sabon tsari da Ganduje ya kaddamar na zuwa ne yayin da ake kokarin tuge shi daga kujerarsa.

A yau Laraba 5 ga watan Yuni wata kotu a jihar Kano ta ba da umarnin tura sammaci ga Ganduje da iyalansa kan zargin badakalar kudi a lokacin da ya ke mulki.

Kara karanta wannan

Tsautsayi ya gitta, Allah ya yiwa babban jami'in ɗan sanda rasuwa yana zaune a ofis

Dr. Ganduje ya sake rokon ƴan Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya sake tura roko ga ƴan Najeriya kan halin da ake ciki.

Ya ce tun yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu duba da matakan da Tinubu ke dauka domin inganta Najeriya.

Ganduje ya kuma ba da tabbacin ci gaba da inganta rayuwar kasar kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya dauki hanya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel