EFCC Ta Taso Kwankwaso Kan Zargin Ya Ci Kuɗin Kamfe? Gaskiya Ta Bayyana

EFCC Ta Taso Kwankwaso Kan Zargin Ya Ci Kuɗin Kamfe? Gaskiya Ta Bayyana

  • Shugaban NNPP na jihar Kano ya musanta rahoton cewa hukumar EFCC ta taso Kwankwaso kan wasu kuɗaɗen kamfe
  • Hashimu Dangurawa ya ce rahoton ƙarya ne kuma wasu maƙiyan Kwankwaso suka kirkiro shi domin ɓata masa suna
  • Ya ce har yanzun jagoran NNPP ne mutun ɗaya tilo da zai iya jan ragamar Najeriya zuwan tudun mun tsira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Shugaban New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ya musanta rahoton cewa EFCC ta taso Rabiu Kwankwaso a gaba.

Dungurawa ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa hukumar yaki da rashawa EFCC ta fara bincikar Kwankwaso kan wasu kuɗin kamfen NNPP.

Kara karanta wannan

EFCC ta fara binciken Sanata Rabi'u Kwankwaso kan zambar kudin 'yan fansho

Rabiu Musa Kwankwaso.
Shugaban NNPP ta musanta rahoton EFCC na binciken Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a birnin Kano, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dungurawa ya bayyana rahotannin da ake yaɗawa a matsayin marasa tushe, inda ya ce Kwankwaso mutum ne amintacce kuma mai gaskiya.

EFCC ta fara binciken Kwankwaso?

Ya ce:

"Mun sha ganin irin wannan jita-jita a lokuta daban-daban kuma ba zamu hana su ba, su ci gaba da yaɗawa.
"Ko sun so ko ba su so, Kwankwaso ne mutum daya tilo da ya rage mai gaskiya, mutunci, farin jini, da gogewar mulkin kasar nan.”

Shugaban NNPP na Kano ya yi fatali da rahoton binciken EFCC, yana mai bayyana shi da labari mara tushe wanda ƴan adawar Kwankwaso suka ƙirƙiro domin ɓata shi.

Su wa ke son ɓata Kwankwaso?

"Rahoton ya fito ne daga maƙiya, jahilai suka yaɗa yayin da wawaye kuma suka yarda. Mun gode Allah da bamu a cikinsu, mu masoyansa ne mun san shi kuma mu ba wawaye ba ne,” inji shi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nuna gwamna 1, ya buƙaci sauran gwamnoni su yi koyi da shi

A cewarsa, wannan rahoton ƙaryar ya taso ne daga ɓangaren masu adawa da Kwankwaso, waɗanda ba su ƙaunar ya zama shugaban ƙasa.

Dungurawa ya tabbatar da cewa babu wani zarge-zargen zamba, rashin da’a, almubazzaranci, ko satar dukiyar al’umma a kan Kwankwaso, rahoton Vanguard.

Matan APC sun yi zanga-zanga

A wani rahoton kuma wasu fusatattun mambobin jam'iyyar APC mata sun mamaye hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a.

Dandazon matan sun gudanar da zanga-zanga ne domin nuna rashin jin daɗinsu da halin shugabar matan APC Mary Alile-Idele.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262