Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Jam'iyyar Kwankwaso Ta Aike da Saƙo Ga Bola Tinubu

Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Jam'iyyar Kwankwaso Ta Aike da Saƙo Ga Bola Tinubu

  • Jam'iyyar NNPP mai kayan maramari ta yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a lokacin da yake cika shekara ɗaya a mulki
  • Uban NNPP, Boniface Aniebonam ya ce tun asali Bola Tinubu ya karɓi kasar nan ne a lokacin da matsaloli suka yi mata katutu
  • Ya bukaci shugaban kasa ya naɗa mutanen kirki a muhimman wurare domin aiwatar da manufar sabunta fata da kawo ci gaba a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar NNPP ta yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da yake murnar cika shekara guda a kan madafun iko.

Uban jam'iyyar NNPP, Dokta Boniface Aniebonam, ya ce shugaban ƙasa ya san ƙalubalen da kasar nan ke fuskanta a lokacin ya karɓi mulki bara.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Tinubu ya bayyana dalilin kai gwamnonin jihohi 36 kotu

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Uban NNPP ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

NNPP ta wanke Shugaba Bola Tinubu

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) game da cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya ranar 29 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta kawo, ya ce ganin irin kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta ne ya sanya shugaban kasar ya fito da manufarsa domin tunkarar matsalolin.

"Shugaba Tinubu mutum ne kamar kowa, ta yiwu akwai wuraren da ya yi kuskure kamar cire tallafin man fetur ba tare da tsara yadda za a magance tasirin ba, amma karshe dai zai zama alheri.
"Don haka wannan lokaci ne da ya kamata ‘yan Nijeriya su kara azama wajen yin aiki tukuru da sadaukarwa domin ci gaban kasarmu."

- Dakta Boniface Aniebonam.

Jam'iyyar NNPP ta yabawa Tinubu

A cewar Aniebonam, Tinubu da ‘yan tawagarsa sun yi nasarar ceto Najeriya daga sashin kula da waɗanda suka kai gargara, ya dawo da ita cikin hayyacinta, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

Ya bukaci shugaban kasar da ya tabbatar ya zaƙulo kwararrun mutane ya naɗa su a muhimman wurare don tafiyar da tsarin sabunta fata domin ci gaban Najeriya.

Uban NNPP ya ce ya kamata Tinubu ya tabbatar da cewa manyan titunan ƙasar nan na cikin yanayi mai kyau domin rage hadurra da sace-sacen mutane da sauran laifuka.

Gwamnatin Jigawa ta ɗauki ma'aikata

A wani rahoton kuma Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnatinsa ta ɗauki sababbin malamai domin cike giɓin da ke akwai a ɓangaren ilimi a jihar Jigawa.

Namadi ya ce ilimi na ɗaya daga cikin manufofi 12 da gwamnatinsa ta sa a gaba da nufin ɗaga darajar jihar ta ƙara ɗaukaka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262