Rikicin Sarauta: Tsagin Ganduje Ya Mayar da Martani Kan Abin da Gwamna Abba Ya Yi a Kano
- Hadimin shugaban APC na ƙasa ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yunƙurin wargaza ayyukan da Ganduje ya yi a Kano
- Cif Oliver Okpala ya ce abubuwan da ke faruwa a Kano wata manaƙisa ce da aka shirya da nufin ganin bayan tsohon gwamna Abdullahi Ganduje
- Wannan kalamai na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan gwamnan Kano ya tsige sarakuna biyar da Ganduje ya naɗa kuma ya dawo da Sanusi II
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - A karon farko tsagin tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje ya yi magana yayin da ake tsaka da rikicin sarauta.
Cif Oliver Okpala, mai magana da yawun shugaban APC ya ce duk wani makirci da ake ƙullawa domin ruguza ayyukan alherin da Ganduje ya zuba a Kano ba zai je ko ina ba.
Ganduje ya tabo Abba kan batun masaratu
Okpala ya ce gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf, ba zai cimma nasara ba a ƙoƙarinsa na shafe dukkan ayyukan raya ƙasa da Ganduje ya aiwatar a lokacin mulkinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya faɗi haka ne a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi kwanaki kalilan bayan Gwamna Abba ya rusa masarautun Kano da Ganduje ya kirkiro, Leadership ta ruwaito.
Gwamna Abba ya kuma dawo da Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano, shekaru huɗu bayan Ganduje ya tsige shi.
Hadimin Ganduje ya soki gwamnan Kano
Da yake mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa a Kano, hadimin Ganduje ya ce kowace gwamnati tana da salon shugabanci amma al'umma za su yi alƙalanci.
A cewarsa, mazauna Kano ne za su yanke ko salon da Abba Kabir ya zo da shi abu ne mai kyau da zai inganta rayuwarsu ko kuma son rai ya zo da shi.
The Sun ta ruwaito Okpala na cewa:
"A lokacin da Ganduje yake mulki ya yi iya kokarinsa, kuma al’ummar jihar Kano za su iya shaida hakan.Ya zuba ayyukan da na bayansa ba zai iya kama ƙafarsa ba.
"Sharri da makircin siyasa ba zasu iya ruguza abubuwan da Ganduje ya yi a Kano cikin dare ɗaya ba domin ayyukan da ya tafi ya bari suna da tarin yawa.
"Don haka wani ya farka dare daya ya yi kokarin ruguza ko wargaza duk wani aiki da magabacinsa ya yi, ba komai bane hakan illa ƙoƙarin illata al’ummar Kano."
Tinubu ya fara gina gidaje 500 a Kano
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta sanya tushen gina gidaje a kauyen Lambu, ƙaramar hukumar Tofa a jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugaban ƙasa bisa yadda ya jajirce domin cike giɓin ƙarancin gidaje a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng