Labour Party Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyyar Na Ƙasa, Julius Abure
- Kwamitin zartarwa na Labour Party reshen jihar Edo ya dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Julius Abure, ba tare da ɓata lokaci ba
- Shugabannin LP na gunduma da ƙaramar hukumar da ya fito sun amince da dakatar da Abure bisa zargin rashin ɗa'a da ladabi
- Jam'iyyar LP ta jihar Edo ta aminta da dakatar da Mista Abure a wani taro da ta gudanar ranar Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Rahotanni daga jihar Edo sun nuna cewa an dakatar da shugaban jam'iyyar LP na ƙasa, Julius Abure, bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.
An tataro cewa kwamitin zartaswa na Labour Party a jihar Edo (SEC) ya amince da matakin dakatar da Abure a wani zama da ya gudana da tsakar daren Jumu'a.
Matakin dakatarwan, wanda ke ƙunshe a wasiƙu biyu masu ɗauke da kwanan watan 14 da 15 ga watan Mayu, zai fara aiki ne nan take, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
LP ta dakatar da Abure
Legit Hausa ta fahimce cewa wasiƙin sun shawarci Mista Abure ya daina ayyana kansa a matsayin a mamban jam'iyyar LP.
Ɗaya daga cikin wasikun dakatarwar na ɗauke da sa hannun shugaban LP na gundumar da Abure ya fito, Thompson Ehiguese da sakatare, Stanley Usiomoh.
A rahoton The Nation, wani sashin takardar ya ce:
"Wannan dakatarwa za ta fara aiki nan take kuma muns baka shawarin ka daina ayyana kanka a matsayin mamban LP a guduma ta 3, Arue, Uromi a ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo."
Abure ya rasa goyon bayan LP
Ana zargin kwamitin zartarwar LP na jihar karkashin jagorancin Kelly Ogbaloi, ya amince da matakin da gunduma da ƙaramar hukumar suka yanke.
Ogbaloi ya ce SEC ba shi da wani zabi illa ya amince da dakatarwar wanda kwamitin zartaswar jam’iyyar ya amince da shi a karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas.
Shi ma da yake nasa jawabin mataimakin shugaban LP a jihar Edo, Patrick Agbontaen, ya ce jam’iyyar ta gaji da irin zarge-zargen da ake yi wa Abure.
PDP ta naɗa kwamitin kamfen Edo
A wani rahoton kuma Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa zai jagoranci kwamitin PDP mai mutane 152 a yakin neman zaben gwamnan Edo.
Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Abuja.
Asali: Legit.ng