Ganduje Ya Bayyana Abubuwan da Ke Yi Wa Mata Barazana a Siyasar Najeriya

Ganduje Ya Bayyana Abubuwan da Ke Yi Wa Mata Barazana a Siyasar Najeriya

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi maganan kan rashin yawan mata ƴan siyasa a Najeriya
  • Ganduje ya bayyana cewa al'adu da addini na daga cikin abubuwan da ke ba mata cikas a harkokin siyasar Najeriya
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana hakan ne lokacin da ya ƙarbi baƙuncin uwargidan mataimakin shugaban ƙasa a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana al’adu da addini a matsayin abubuwan da ke kawo cikas ga ɗumbin mata a harkokin siyasar Najeriya.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 22 ga watan Mayun 2024 a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya wanke Tinubu daga zargin wuyar da ake sha a Najeriya

Ganduje ya fadi abubuwan da ke ba mata cikas a siyasa
Ganduje ya yi magana kan abubuwan da ke ba mata cikas a siyasar Najeriya Hoto: @officialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa tsohon gwamnan na jihar Kano ya karɓi baƙuncin uwargidan mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima, wacce ta kai ziyara sakatariyar jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uwargidan mataimakin shugaban ƙasar ta kai ziyarar ne tare da matan manyan ƴan siyasa domin ƙarfafa gwiwar mata a jam’iyyar.

Wane jawabi Ganduje ya yi gaban mata?

"Yawan mata a Najeriya ya zarce yawan maza. Za ka ga idan ana maganar zaɓe, mata sun fi jajircewa ko mai zafi, sanyi, ƙura za su tsaya su yi zaɓe."
"Amma idan ana maganar rabon nasarar zaɓen, maza ne suke mamaye komai. Dole ne mu canja hakan domin ƙara yawan shigar mata cikin siyasa."
"Ko da yake akwai abubuwa na al'adu, akwai abubuwa na addini, zuwa wani lokaci, duk waɗannan za su kauce domin mata su shiga a dama da su sosai a siyasa. Hakan zai inganta tattalin arzikin matanmu matuƙa."

Kara karanta wannan

'Yan APC sun fadi wadanda suka sanya su yin zanga-zangar adawa da Ganduje

- Abdullahi Umar Ganduje

A nata jawabin, Nana Shettima, wacce ta ce ita ce ta wakilci uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta roki ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnati, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Ganduje ya samu muhimmiyar shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ba shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, shawara kan rikicin jam'iyyar.

Abbas Tajudeen ya buƙaci Ganduje da ya kafa kwamitocin sulhu da za su haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar da ke rikici da juna a faɗin ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng