Ganduje: Wasu Ƴan Arewa Sun Kunno Wuta Kan Kujerar Shugaban APC Na Ƙasa
- Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na ci gaba da fuskantar adawa daga yankin Arewa ta Tsakiya
- Kungiyar ƴaƴan APC sun fara neman goyon baya domin kwato kujerar shugaban jam'iyyar APC daga hannun Ganduje
- A cewar shugaban ƙungiyar, ba za wu yi ƙasa a guiwa ba wajen dawo da kujerar kuma tuni suka kai ƙara gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wata kungiyar mambobin jam'iyyar APC a Arewa da Tsakiya ta yi kira ga masu faɗa a ji na shiyyar su fito su mara mata baya wajen kwato kujerar shugaban jam'iyya mai mulki.
Ƙungiyar ta nemi fitattun ƙungiyoyi kamar lauyoyi da ƙungiyoyin fararen hula su haɗa kai domin sauke Dakta Abdullahi Ganduje daga kujerar shugaban APC na ƙasa.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Saleh Mandung Zazzaga, ne ya yi wannan kira yayin zantawa da manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kujerar da Ganduje ke zaune a kai ta shiyyar Arewa ta Tsakiya kamar yadda jam'iyyar APC ta tsara, cewar rahoton jaridar Leadership.
Alhaji Sale ya ce kamata ya yi wani ɗan jihar Nasarawa ko ɗan Arewa ta Tsakiya ya maye gurbin Abdullahi Adamu amma ba Ganduje ba wanda ya fito daga Arewa maso Yamma.
Ganduje na fuskantar matsala
Ya ƙara da cewa gundumar Ganduje a jihar Kano ta kaɗa masa ƙuri'ar rashin amincewa da dakatar da shi, sannan kuma an shigar da Ganduje ƙara a kotu.
Shugaban ƙungiyar ta APC ya ce saboda haka ne suka fito suka fara neman a dawo masu da kujerar shugaban jam'iyya wadda aka ƙwace da ƙarfi.
A cewarsa, wannan dalilin ne ya sa suke neman fitattun ƙungiyoyi su haɗa kai da su domin cimma nasara a wannan kudiri da suka sanya a gaba.
Ya ce ba a APC kaɗai ba, duk inda suka ga za a mayar da Arewa ta Tsakiya saniyar ware, ko a yaudari yankin, sai inda ƙarfinsu ya ƙare, Daily Post ta tattaro.
Zazzaga, mamban kwamitin kamfen shugaban kasa a zaben da ya gabata ya ce za a ci gaba da sauraron karar da kungiyar ta shigar da Ganduje a ranar 30 ga watan Mayu.
Jerin ministocin Tinubu da suka fi ƙoƙari
A wani rahoton kuma Deji Adeyanju, mai fafutukar kare hakkin ɗan adam ya tantance ministocin da suka fi ƙoƙari da marasa amfani a Gwamnatin Bola Tinubu.
Adeyanju ya raba ministocin zuwa rukuni biyu, jerin masu koƙari da kuma rukunin ƴan zaman dumama kujera bisa la'akari da ayyukansu.
Asali: Legit.ng