29 Ga Mayu: An Jero Sunayen Ministocin da Suka Fi Ƙoƙari da Mafi Lalacewa a Mulkin Tinubu
- Deji Adeyanju, mai fafutukar kare hakkin ɗan adam ya tantance ministocin da suka fi ƙoƙari da marasa amfani a Gwamnatin Bola Tinubu
- Adeyanju ya raba ministocin zuwa rukuni biyu, jerin masu koƙari da kuma rukunin ƴan zaman dumama kujera bisa la'akari da ayyukansu
- Ya zaɓi ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo a matsayin wanda ya fi ƙokari yayin ministan wutar lantarki, Adelabu ya fi muni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ɗan gwagwarmayar kare hakkin ɗan adam kuma shugaban ƙungiyar ƴan Najeriya masu kishi, Deji Adeyanjo, ya bai wa ministoci maki a mulkin Bola Tinubu.
Mista Adeyanju ya duba ayyukan da kowane minista ya yi wajen tantance koƙarinsa yayin da ake tunkarar ranar demokuraɗiyya, 29 ga watan Mayu, 2024.
Jerin ministocin da suka fi ƙoƙari
Ya bayyana Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida a matsayin wanda ya fi kowane minista ƙoƙari a gwamnatin shugaban ƙasa Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan gwagwarmayar da ke zaune a Abuja ya sanya ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a matsayin minista na biyu da ya fi ƙoƙari a gwamnati mai ci.
Ministan ayyuka, Dave Umahi, shi ne ya ɗare a matsayi na uku a jerin ministocin da suka fitar da Tinubu kunya in ji Adeyanju.
Ya bayyana haka ne a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Jumu'a, 17 ga watan Mayu, 2023.
A rukunun mafi munin ministoci waɗanda ba su taɓuka komai ba Adeyanju ya sanya ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu a matsayi na daya.
Ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Olawale Edun, shi ne ya zo na biyu a jerin ministocin da suka bai wa ƴan Najeriya kunya.
Deji Adeyanju ya wallafa a shafinsa cewa:
"Ministocin da suka fi kokari a gwamnatin Tinubu - Tunji Ojo a matsayi na farko, Nyesom Wike na biyu da Dave Umahi a matsayin na uku.
"Ministoci mafi muni kuma sune, Adelabu na farko, Wale Edun na biyu, wa kuke ganin zai zama na uku?"
Ƴan Najeriya sun faɗi ra'ayoyinsu
Oluwafemi @allstarmGr ya ce:
"Ɗan uwa ina ka baro Oyetola? Wannan mutumin ba abin da yake yi a matsayin minista."
Snappy @Litkwalssnappy ya ce:
"Mafi lalacewar ministoci, Adelabu na ɗaya, Oyetola na biyu."
Rótìmí @trooye ya ce:
"A ganina Wale Edun ne zai ɗauki na ɗaya da na biyu da na uku (a ministocin da ba su da amfani). Ku kyale Adelabu shi lalacewarsa ta musamman ce."
Atiku ya yi magana kan zaɓen 2027
A wani rahoton kuma Alhaji Atiku Abubakar ya ce mambobin PDP ne kaɗai za su yanke wanda za a ba tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi bayanin ganawarsa da Peter Obi da kuma shirin da suka fara domin tunkarar zaɓe na gaba.
Asali: Legit.ng