Tsohon Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP a jihar Osun a karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta rasa ɗaya daga cikin manyan kusoshinta
  • Alhaji Shuaib Oyedokun ya fice daga PDP kamar yadda ya bayyana a wasiƙar da ya miƙa wa shugannin jam'iyyar na Osun ranar Alhamis
  • Oyedokun, tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda an sauka daga aƙidar da aka kafa jam'iyyar tun usuli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya samu tangarɗa yayin da ɗaya daga cikin abokansa na siyasa kuma babban jigon PDP ya sauya sheƙa zuwa APC.

Alhaji Shuaib Oyedokun, tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa ya fice daga jam'iyyar kuma ya sanar da cewa ya rungumi jam'iyyar APC ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Jita-jita ta yawaita yayin da Peter Obi ya gana da tsohon gwamnan jihar Jigawa

Adeleke da Oyedokun.
PDP ta rasa babban jigo a jihar Osun, Oyedokun ya koma APC Hoto: Shu'aib Oyedokun, Osun PDP
Asali: Facebook

Oyedokun ya faɗi dalilin komawa APC

Kamar yadda jaridar Punch ta kawo, Oyedokun ya bayyana cewa ya ɗauki matakin sauya sheka daga PDP zuwa APC ne bayan tattaunawa da magoya bayansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen ɗan siyasar ya ce zai koma tafiyar APC ne saboda yana ganin a can ne za a martaba gogewarsa a siyasa kuma a yabawa kokarinsa da iya shugabanci.

A wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan watan 16 ga watan Mayu, Oyedokun ya ce gurɓata aƙidun da aka kafa PDP na ɗaya daga cikin abin da ya ja hankalinsa ya bar jam'iyyar.

PDP ta rasa shugabanta zuwa jam'iyyar APC

Ya tura wasiƙar murabus ɗinsa daga PDP zuwa shugaban jam'iyya na ƙasa ta hannun shugabannin jam'iyyar na gunduma, ƙaramar hukuma da kuma jihar Osun, Tribune Nigeria ta tattaro.

"Bayan tuntuɓar ɗumbin magoya bayana, na yanke shawarar ɗaukar matakin sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC, inda nake tunanin za a martaba ni kuma a yaba wa ƙoƙarina."

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, SGF Akume ya karɓe shi a Abuja

- Alhaji Shuaib Oyedokun

Jiga-jigan PDP na shirin komawa APC

Wannan sauya sheka ta Oyedokun na zuwa a lokacin da ɗan takarar gwamnan da ya marawa baya a zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar PDP a 2022 ke shirin shiga APC.

Jam'iyyar APC ta jihar Osun ta ce Dokta Dotun Babayemi da magoya bayansa za su baro PDP zuwa APC a wani rali da aka shirya ranar Jumu'a, 17 ga watan Mayu.

PDP v LP: Atiku ya gana da Peter Obi

A wani rahoton kuma manyan ƴan takarar shugaban ƙasa a 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun gana yayin da ake shirin zaɓen 2027.

Atiku wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne ya ce abin alfahari da girma ne da ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Anambra, Obi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel