A Ƙarshe, Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Sahihancin Zaɓen Gwamnan Jihar Kogi

A Ƙarshe, Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Sahihancin Zaɓen Gwamnan Jihar Kogi

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi ta tanadi hukunci kan sahihanci zaɓen Gwamna Ahmed Ododo
  • A zaman kotun na ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, kotun ta ce za ta sanar da ranar da za a dawo domin yanke hukunci nan gaba
  • Jam'iyyar SDP da ɗan takararta na gwamna, Murtala Ajaka ne suka kalubalanci nasarar APC a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Kogi da ke zama a Abuja ta shirya yanke hukunci kan sahihanci nasarar Gwamna Ahmed Usman Ododo.

Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) da ɗan takararta na gwamna, Murtala Ajaka ne suka shigar da karar ƙalubalantar nasarar Gwamna Ododo na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga muhimmin taro a Villa, ya rantsar da sababbin kwamishinoni 2

Ajaka da Ododo.
Kotun zaɓe ta shirya yanke hukunci kan ƙarar zaben gwamnan jihar Kogi Hoto: Murtala Ajaka, Ahmed Usman Ododo
Asali: Twitter

A zaman ranar Litinin, kotun zaɓen ta tanadi hukunci bayan kammala sauraron bayanan kowane ɓangare, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC, Ododo da APC sun nemi a kori ƙarar

Yayin zaman shari'ar na ƙarshe, hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), jam'iyyar APC da Gwamna Ododo sun roƙi kotun tayi watsi da ƙarar Ajaka saboda ba ta da wurin zama ba.

Sun bayyana haka ne ta hannun lauyoyinsu, Kanu Agabi, Joseph Daudu da kuma Emmanuel Ukala yayin miƙa takardar bayanan karshe.

Lauyan Ajaka, Pius Akubo, ya bukaci kotun da ta ajiye abubuwan da Ododo ya gabatar a gefe tare da tabbatar da waɗanda suka gabatar mata.

Bayan sauraron dukkan bangarorin, kotun zaɓen karkashin Mai shari’a Ado Birnin-Kudu, ta tanadi hukunci, inda ta ce za ta sanya ranar da za a dawo domin karanto hukuncin.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta matashi mai karyar ya shigo musulunci daga Kiristanci a Kano

Ododo ya zama gwamnan jihar Kogi

Tun da farko dai INEC ta bayyana Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar ranar 11 ga Nuwamba, 2023.

Ododo, na hannun damar tsohon Gwamna Yahaya Bello ya samu kuri’u 446,237, ya doke abokin hamayyarsa Ajaka na SDP wanda ya samu kuri’u 259,052, yayin da Dino Melaye na PDP ya samu kuri’u 46,362.

Ododo da Melaye sun ce zaben cike yake da da kura-kurai. Daga baya dan takarar SDP ya kalubalanci sakamakon zaben a kotu, rahoton The Cable.

Hadi Sirika zai sake gurfana a kotu

A wani rahoton kuma hukumar EFCC za ta sake gurfanar da ministan sufurin jiragen sama a lokacin mulkin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika a gaban kotu.

Sirika tare da ɗan uwansa za su gurfana a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja yau Talata kan wasu tuhume-tuhume shida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262