Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Yi Rashin Nasara a Babbar Kotun Tarayya
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi rashin nasara a yunkurin dakatar da shari'ar da ake masa kan badakalar N80bn
- Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan saboda bai halarci zaman shari'a ba ranar Jumu'a
- Alkalin kotun ya caccaki Yahaya Bello da lauyansa kan rashin zuwan wanda ake tuhuma, ya ce EFCC hukuma ce mai bin doka da oda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a zamanta na ranar Jumu'a.
Alkalin kotun mai shari'a Emeka Nwite ya yi fatali da buƙatar tsohon gwamnan wanda ya nemi a dakatar da shari'ar da ake masa kan badaƙalar N80bn.
Bello ya bukaci alkalin ya dakatar da sauraron shari’ar da ake yi masa, bisa dalilin karar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki ta'adi (EFCC) ta shigar kan zargin cin mutuncin shugabanta, Ola Olukoyede.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta watsar da buƙatar Yahaya Bello
Da yake yanke hukunci kan wannan buƙata mai shari'a Nwite ya ce kotu ba za ta saurari batun ba har sai wanda ake ƙara ya gurfana a gabanta, Premium Times ta ruwaito.
"Ba za a saurari buƙatar ba har sai wanda ake tuhuma ya halarci zaman kotu, amma tun da wanda ake ƙara baya nan, ƙorafin ba zai karɓu ba."
Da yake sukar Yahaya Bello da lauyansa, alkalin ya ce tsohon gwamnan na kokarin bata tsarin shari’a ne ya hanyar ƙin gabatar da kansa a gaban ƙotu.
"Kai ne kake zuga wanda ake tuhuma, menene abin da kuke tsoro? Mutum nawa kuka taɓa jin an ce hukumar EFCC ta kashe? EFCC hukuma ce mai bin doka sau da ƙafa."
"Shin wanda ka ke karewa ne kaɗai tsohon gwamnan da EFCC ta gayyata? Ka kawo shi kotu, ni kuma zan saurari buƙatarka,” in ji alkalin.
Yahaya Bello zai gurfana a kotu
Biyo bayan kin dakatar da shari’ar da kotu ta yi, Mista Bello ya yi alkawarin mika kansa domin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed, ya dauki nauyin gabatar da wanda yake karewa a gaban kotu a ranar 13 ga watan Yuni, The Cable ta ruwaito.
Fubara ya canza wurin zaman majalisa
A wani rahoton na daban yayin da rikicin jihar Ribas ke ƙara tsananta, Gwamna Fubara ya canza wurin zaman majalisar dokokin jihar Ribas.
A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Disamba, 2023, gwamnan ya ce an ɗauke matakin ne saboda babu tsaro a zauren majalisar.
Asali: Legit.ng