Gwamna Sule Ya Faɗi Matsayar Gwamnonin Jihohi Game da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamna Sule Ya Faɗi Matsayar Gwamnonin Jihohi Game da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

  • Gwamnonin jihohin Najeriya sun damu da walwalar ma'aikata kuma ba su adawa da sabon mafi ƙarancin albashi
  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ne ya bayyana haka a Aso Villa jim kaɗan bayan ganawa da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima
  • Ya ce duk da ba shi da hurumin magana da yawun gwamnoni amma ya san cewa suna jiran kwamitin mafi ƙarancin albashi ya gama aikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa shi da sauran gwamnonin jihohin ƙasar sun damu matuƙa da walwalar ma'aikata.

Abdullahi Sule ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da masu ɗauko rahoto a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"Ba za su iya ba": Sanata Ibrahim ya jero ministocin da ya kamata Bola Tinubu ya kora

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce gwamnoni suna dakon kwamitin mafi ƙarancin albashi ya gama aikinsa Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Twitter

Gwamna Sule ya tabo batun karin albashi

Mai girma gwamnan ya yi magana ne jim kaɗan bayan ganawa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a gidan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce gwamnoni ba su adawa da yunƙurin samar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Albashin da gwamnonin jihohi suke biya

Sule ya ce jihar Nasarawa ta fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 tun a shekarar 2019 kuma tana samar da ƙarin tagomashi kala daban-daban ga ma'aikata.

Ya ƙara cewa bai san wata jiha da gwamnatin jihar ba za ta iya biyan mafi karancin albashi na N30,000 ba.

Albashi: Matsayar da gwamnoni suka ɗauka

"Mun damu da walwalar ma'aikata, muna biyan wani alawus na musmaman da ake kira 'Hazard' ga ma'aikatan lafiya. Saboda haka bana tunanin gwamnoni suna da matsala da biyan mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dauki mataki bayan kwashe kwanaki a kauyen da aka kashe jami'ai

"Ba ni ke magana da yawun gwamnoni ba, shugaban mu kuma gwamnan jihar Kwara ne ke da wannan iko kuma na san zai fito ya yi ƙarin haske a lokacin da ya dace."
"Amma kuskure ne a ce gwamnoni ba su son a yi sabon mafi ƙarancin albashi ko sun ƙi bada haɗin kai. Abin da gwamnoni ke ƙara nanatawa shi ne an kafa kwamitin da ke aikin.

- Abdullahi Sule.

Gwamna Sule ya ƙara da cewa a yanzu suna jiran wannan kwamiti ya gama aikinsa kan mafi ƙarancin albashi domin a ɗauki mataki na gaba, rahoton Guardian.

Sanata ya nemi Tinubu ya kori ministoci

A wani labarin, Sanata Jimoh Ibrahim ya shawarci Bola Ahmed Tinubu ya tashi tsaye, ya sallami wasu daga cikin ministocinsa saboda ba zasu iya ba.

Ibrahim, mamban kwamitin kasafi na majalisar dattawa ya koka cewa Tinubu ya ɗauko wasu mutane da ake zargi da cin hanci ya ɗora a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262