"Ku Daina Tsoma Baki a Gwamnatina" Gwamna Ya Gargaɗi Tsofaffin Gwamnoni
- Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya gargaɗi tsofaffin gwamnonin jihar su daina tsoma baki kan harkokin gwamnatinsa
- Alia ya bayyana cewa ba zai bar wasu mutane daga gefe su kawo masa tangarda da rabuwar kai ba tun da sun gama wa'adinsu
- Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Samuel Ortom ya shawarci Alia ya yi taka tsan-tsan da masu kokarin haɗa shi faɗa da Akume
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Alia, a ranar Juma’a, ya bukaci tsoffin gwamnonin jihar da suka gabace shi su guji tsoma baki a harkokin gwamnatinsa.
Gwamna Hyacinth Alia ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi jim kaɗan bayan dawowa daga kasar Amurka, Ripples Nigeria ta rahoto.
Ortom ya magantu kan Gwamnatin Alia
Duk da gwamnan bai ambaci sunan kowa ba kai tsaye amma ana hasashen yana martani ne ga tsohon gwamnan da ya gada, Samuel Ortom, jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun farko, a wurin bikin cikarsa shekara 63, Ortom ya ja hankalin Alia cewa duk waɗanda ke ba shi shawarar faɗa da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ba su ƙaunar jihar Benuwai.
Gwamma Alia ya gargaɗi Ortom
Amma da yake zantawa da ƴan jarida a Makurdi, Gwamna Alia ya ja kunnen magabatansa daga yanzu kar wanda ya sake sa masa baki a gwamnatinsa.
Gwamnan ya bayyana cewa ba zai bari wani can ya zo ya kawo rarrabuwa a gwamnatinsa ba.
"Ba zan bar kowa ba; tsohon gwamna ko ma'aikacin gwamnati, idan kai tsohon gwamna ne kuma ba zaka iya ba da gudummuwar komai ga jihar Benuwai ba, ka rufe mana baki.
"Kun gama naku mulkin don haka ku san me za ku faɗa, muna maraba da sukar ƴan adawa amma ku riƙa tabbatar da abin da bakinku zai faɗa.
"Tun da kun gama wa'adin mulkin ku ba zai yiwu ku dawo kuna kokarin wargaza wannan gwamnatin ba."
- Gwamna Alia.
Jigo ya fice daga jam'iyyar APC
A wani rahoton jigon APC a jihar Edo ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP yayin da ake shirin zaɓen gwamna a watan Satumba mai zuwa.
Honorabul Ogini Kingsley Topa ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin marawa Gwamna Obaseki baya a ƙoƙarinsa na kawo ci gaba.
Asali: Legit.ng