Ba a Gama Batun Dakatarwa ba, An Taso Ganduje a Gaba Sai Ya Yi Murabus a APC
- Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da suka fito daga shiyyar Arewa ta Tsakiya sun buƙaci shugaban jam'iyyar na ƙasa ya yi murabus daga muƙaminsa
- Jiga-jigan sun yi nuni da cewa zaman Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban APC na ƙasa ya saɓawa kundin tsaron mulkin jam'iyyar
- Sun nuna damuwa kan yadda aka mayar da shiyyarsu saniyar a wajen rashin samun muƙamai masu gwaɓi a jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya sun aika da wasiƙa zuwa ga kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na APC.
Jiga-jigan na APC a cikin wasiƙar ta su sun buƙaci shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Jaridar Daily Trust ta ce Mohammed Mahmud Saba shi ne ya rattaɓa hannu kan wasiƙar mai taken "ƙuri'ar rashin amincewa tare da neman cire Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban APC na ƙasa".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed Mahmud Saba ya ce saɓanin nuna amincewa da Ganduje da shugabannin APC suka yi, al'ummar shiyyar Arewa ta Tsakiya na neman ya yi murabus.
Meyasa ake son murabus ɗin Ganduje?
Mohammed ya yi nuni da cewa zaman Ganduje shugaban APC na ƙasa ya saɓawa kundin tsarin mulkin APC, saboda an yaudari yankin Arewa ta Tsakiya da ya kamata ya samar da shugaba bayan murabus ɗin Abdullahi Adamu.
Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:
"Shiyyar Arewa ta Yamma inda Ganduje ya fito suna da kakakin majalisar wakilai, mataimakin shugaban majalisar dattawa, shiyyar Arewa ta Gabas suna da mataimakin shugaban ƙasa da mataimakin shugaban APC na ƙasa (Arewa)"
"Amma shiyyar Arewa ta Tsakiya wanda sakataren gwamnatin tarayya kawai aka ɗauka ya kamata ta samar da kujerar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa.
"Saboda haka muna gabatar da waɗannan buƙatun, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus sannan ya daina kiran kansa a matsayin shugaban jam'iyyar mu."
"A mutunta tsarin karɓa-karɓa da aka amince da shi a lokacin babban taron APC na shekarar 2022 wanda ya kai kujerar shugaban jam'iyyar na ƙasa shiyyar Arewa ta Tsakiya."
Masu hannu a dakatar da Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin jihar Kano ce ke da hannu a dakatarwar da aka yi masa daga APC.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi nuni da cewa ko kaɗan bai damu da dakatarwar da aka yi masa ba wanda ya zargi gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kitsawa.
Asali: Legit.ng