Watanni 2 Bayan Rantsuwa, Gwamnan PDP Ya Tura Sunayen Sababbin Kwamishinoni 14 Ga Majalisa

Watanni 2 Bayan Rantsuwa, Gwamnan PDP Ya Tura Sunayen Sababbin Kwamishinoni 14 Ga Majalisa

  • Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP ya naɗa sababbin kwamishinoni 14 a gwamnatin jihar Bayelsa
  • A wata takarda da ya rattaɓawa hannu, Gwamna Diri ya aike da sunayen waɗanda ya naɗa zuwa majalisar dokokin jihar
  • Ana sa ran ranar Alhamis mai zuwa sababbin kwamishinonin za su bayyana a gaban majalisar domin tantancewa da tabbatar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya aike da sunayen sababbin kwamishinoni 14 ga majalisar dokoki domin tantance su da tabbatar da naɗin su.

Hakan na kunshe ne a wata takarda da gwamnan ya yi wa take da, "tura sunayen kwamoshinoni," wadda ke ɗauke da adireshin shugaban majalisar dokokin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Gwamna Douye Diri.
Watanni 2 bayan rantsar da shi, Gwamna Diri ya naɗa kwamishinoni Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa takardar dai na ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Afriu da sa hannun Gwamna Diri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Diri ya rubuta cewa:

"Digaro da sashe na 192 na kundin tsarin mulkin Najeriya (wanda aka gyara), ina mika waɗannan sunayen ga majalisa domin ta amince da su a matsayin kwamishinonin gwamnatin jihar Bayelsa.”

Jerin sunayen kwamoshinoni 14

Daga cikin mutane 14 da ya nada har da tsofaffin kwamishinoni takwas da gwamnan ya sake nada su, wadanda suka yi aiki a wa'adin farko na gwamnatinsa.

Tsofaffin kwamishinonin da Gwamna Diri ya sake dawo da su sune, Dambo Biriyai, SAN; Maxwell Ebibai, Moses Teibowei, Daniel Igali, Gentle Emelah, Ayibakipreye Broderick, George Flint da kuma Jones Ebieri.

Sauran sabbabin da ya naɗa kuma sun haɗa da Misis Koku Obiyai, Komuko Akari, Perepuighe Biewari, Peter Afagha, Misis Elizabeth Bidei da kuma Michael Magbisa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, sun tafka ɓarna a jihar Arewa

Yaushe za a tantance su?

Wannan jerin sunayen kwamishinonin na zuwa ne watanni biyu bayan rantsar da Diri a matsayin gwamna karo na biyu a ranar 14 ga Fabrairu, 2024.

Ana sa ran wadanda aka nada a matsayin kwamishinonin za su gurfana gaban majalisar ranar Alhamis mai zuwa domin tantance su, The Nation ta ruwaito.

Gwamna Aiyedatiwa ya shiga matsala

A wani rahoton na daban Wasu shugabannin APC a jihar Ondo sun zargi Gwamna Lucky Aiyedatiwa da aikata babban laifi gabanin zaɓen fitar da ɗan takara.

Daga cikin abubuwan da suka zargi gwamnan, jagororin APC sun yi iƙirarin cewa Aiyedatiwa ya fara buga katunan zama mamban jam'iyya na bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262