Mataimakin Gwamnan da Aka Tsige Ya Mayar da Martani Mai Zafi, Ya Tona Wani Sirri
- Tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu, ya mayar da martani bayan majalisar dokokin jihar ta tsige shi ranar Litinin
- Shaibu ya godewa ɗaukacin al'ummar jihar Edo bisa goyon bayan da suka nuna masa yayin da yake fama da jarrabawa mai wahala
- A wani jawabi da ya yi, wanda Legit Hausa ta ci karo da shi, Shaibu ya ayyana tsigewar da aka yi masa a matsayin 'haramtacciya'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo da ka tsige, Philip Shaibu, ya mayar da martani kan matakin da majalisar dokokin jihar ta ɗauka a kansa.
Shaibu ya bayyana tsige shi da majalisar dokokin ta yi daga kan kujerar mataimakin gwamna a matsayin wanda ya saɓa doka.
Ya ce tuhume-tuhume da aka rataya masa da suka haɗa da ƙarya da kuma fallasa asirin gwamnatin jihar Edo duk wani tuggu ne da aka shirya masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamared Shaibu ya faɗi haka ne a wani faifan bidiyo mai mintuna 4 da daƙiƙu 50 wanda ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024.
A cewarsa, wannan mataki na tsige shi koma baya ne ga tsarin demokuraɗiyya, inda ya ƙara da cewa an kitsa masa wannan tuggun ne saboda burinsa na takarar gwamna.
Wane mataki Shaibu zai ɗauka?
A kalamansa, Shaibu ya ce:
"Mutanen jihar Edo, ina mai gode muku bisa yadda kuka tsaya tare da ni a wannan yanayi mara daɗi a matsayina na mataimakin gwamnan jihar Edo.
“Na yi Allah-wadai da matakin tsigewa ba bisa ka’ida ba da majalisar dokokin jihar Edo ta ɗauka a kaina kan wasu tuhume-tuhume.
"Ba ni ake hari ba, tsarin demokuradiyyar da muke mutuntawa ake hari. Wannan lamari alama ce ta mulkin kama karya da kuma barazana da tubalin demokuraɗiyya.
"Ina da yaƙinin ɓangaren shari'a zai mun adalci tare da tona asirin makircin da aka kitsa mun," in ji shi.
An naɗa sabon mataimakin gwamna
A wani rahoton kuma Gwamna Obaseki na jihar Edo ya ɗauki sabon mataimakin gwamna jim kaɗan bayan majalisar dokoki ta tsige Kwamred Philip Shaibu.
Bayanai sun nuna cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen rantsar da Marvellous Omobayo Godwin a gidan gwamnati da ke Benin ranar Litinin.
Asali: Legit.ng