Miyagu Sun Farmaki Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar Arewa Yayin da Halarci Taro a Mazaɓarsa
- Wasu ƴan daba da ake zargin turo su aka yi sun farmaki ɗan majalisar wakilan tarayya, Cif Philip Agbese a jihar Benuwai
- Ganau ya bayyana cewa ƴan daban dauke da makamai sun farmaki ɗan majalisar ne a wurin taron bikin Easter a mazaɓarsa
- Zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun kama wasu daga cikin ƴan daban yayin da suka fara bincike kan lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Tsagerun ƴan daba sun farmaki mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Ado/Okpokwu/Ogbadibo ta jihar Benuwai, Cif Philip Agbese.
Lamarin ya faru ne a lokacin da yake gudanar da wasu harkoki a a mazabar Igumale, hedikwatar karamar hukumar Ado a jihar Benue a ranar Alhamis.
Wani ganau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa The Nation cewa Agbese, yana gudanar da shagulgulan Easter tare da mambobin mazabarsa lokacin da aka farmake shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ana cikin taron bikin Easter kwatsam wasu matasa dauke da mugayen makamai kamar wukake, sanduna, da adduna suka kutsa kai suka tarwatsa taron.
Bayanai sun nuna cewa da kyar ɗan majalisar ya tsira daga sharrin ƴan daban yayin da jami'an tsaro suka yi ƙoƙari suka bar wurin da shi ba tare da an jikkata shi ba.
Jami'an tsaro sun ɗauki mataki
Bugu da ƙari, jami'an tsaro sun yi nasarar kama wasu daga cikin ƴan daban kuma tuni suka fara bincike domin gano dukkan masu hannu.
Har zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton ba a samu jin ta bakin ɗan majalisar tarayya, Mista Agbese, kan lamarin ba.
Amma manyan mutane ƴan asalin yankin ƙaramar hukumar Ado sun yi tir da harin da aka kai wa ɗan majalisar, a cewarsu wasu ne suka ɗauki nauyin ƴan daban.
Jihar Benuwai na fama da rigingimun siyasa a ƴan kwanakin nan musamman a jam'iyyar APC mai mulki, cewar rahoton Independent.
Yan bindiga sun kai hari a Kogi
A wani rahoton kuma wasu ƴan bindiga da ba a sani ba sun farmaki kauyen Agojeju-Odo da ke jihar Kogi, sun halaka mutane da yawa kuma sun ƙona gidaje.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce CP ya tura karin jami'an ƴan sanda.
Asali: Legit.ng