Gwamnan PDP Ya Ba da Hutun Kwana 1 Saboda Muhimmin Abu, Bayanai Sun Fito
- Ma'aikata za su samu damar ba da gudummuwa a zaben kananan hukumomin da za a yi a jihar Bayelsa ranar Asabar mai zuwa
- Gwamna Douye Diri ya sanar da ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu a matsayin ranar hutu ga dukkan ma'aikatan gwamnati na jihar
- Shugaban ma'aikata a Bayelsa, Biobelemoye Charles-Onyema ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya bayyana ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan gwamnati.
Gwamna Diri ya ba da hutu ne domin bai wa ma'aikatan damar komawa gida, kana su kaɗa kuri'a a zaɓen kananan hukumomin jihar da za a yi ranar Asabar 6 ga watan Afrilu.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban ma'aikata, Biobelemoye Charles-Onyema, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma sanarwar ta bayyana cewa wannan hutun bai shafi ma'aikatan gwamnati da ke tafiyar da ayyuka na musamman ba.
Yayin da ya rage saura sa'o'i kaɗan a fafata zaɓen kananan hukumomin, har yanzun jam'iyyun siyasa ba su tsayar da ƴan takara ba.
A rahoton Vanguard, jam'iyyar PDP ce kaɗai ta fitar da ƴan takararta a zaɓen na ranar Asabar, amma har yanzu jam'iyyun adawa sun yi shiru.
Gwamna Diri ya naɗa SSG, CoS da CPC
Tun farko dai Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa Gwamna Diri ya naɗa Farfesa Nimibofa Ayawei a matsayin sakataren gwamnatin jihar Bayelsa.
Haka nan kuma gwamnan ya amince da naɗin Peter Pereotubo Akpe a matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatinsa a ranar Talata, 26 ga watan Maris.
Bugu da ƙari, Diri ya amince da naɗin Irorodamie Komonibo a matsayin mataimakin shugaban ma'aikata, kana ya riƙe Daniel Alabrah a matsayin sakataren watsa labarai.
Dukkan waɗannan naɗe-naɗe na kunshe a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Alabrah ya fitar.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Diri ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Bayelsa karo na biyu bayan ya samu nasara a watan Nuwamba.
An ba Shaibu damar ƙarshe
A wani rahoton na daban, kwamitin bincike ya bai wa mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamred Philip Shaibu dama ta karshe ya bayyana domin kare kansa.
Babban alƙalin jihar Edo ya kafa kwamitin mai mutum bakwai domin bincikar zargin da ake wa Shaibu wanda majalisa ke shirin tsigewa.
Asali: Legit.ng