"Ba Za Ta Saɓu Ba" Gwamnan APC Ya Yi Fatali da Naɗin Hadimai Sama da 270 Kan Abu 1

"Ba Za Ta Saɓu Ba" Gwamnan APC Ya Yi Fatali da Naɗin Hadimai Sama da 270 Kan Abu 1

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi fatali da naɗe-naɗen hadimai sama da 270 wanda Antoni Janar na jihar Ondo ya yi
  • Tun farko dai kwamishinan shari'a, Olukayode Ajulo, ya ce ya naɗa lauyoyi 273 a matsayin masu ba shi shawara domin inganta ayyukan shari'a a Ondo
  • Amma a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan ya fitar, ya ce ba za a biya hadiman daga baitul malin jihar ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce ba zai biya lauyoyi 273 da Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a, Olukayode Ajulo ya nada a matsayin hadimai ba.

Kamar yadda The Nation ta tattaro, kwamaishinan ya naɗa lauyoyi 273 a matsayin mataimakansa na musamman a harkokin shari'a a jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Gwamnan Ondo ya ƙi aminta da nade-naden kwamishinan shari'a Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Meyasa kwamishinan ya yi naɗi mai yawa?

Mista Ajulo ya bayyana cewa ya naɗa su ne domin aiwatar da aiki mai inganci, dogaro da kai da tabbatar da ɗa'a a jihar Ondo tare da kare haƙƙin al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Antoni Janar ya ƙara da bayanin cewa lauyoyin suna da gogewa kuma ya amince da naɗinsu, inda ya ce wasu naɗin girmamawa ne yayin da wasu mashawarta na fasaha ne.

"Zasu taimaka wajen jan ragamar ofishin antoni janar na jihar Ondo ta yadda zai zama ofishin shari'a mafi kyau a Najeriya," in ji shi.

Gwamna ya yi fatali da lauyoyin

Amma Gwamna Aiyedatiwa ya yi fatali da lauyoyin da Antoni Janar ya naɗa a matsayin hadimai, inda ya ce gwamnati ba zata biya su albashi ba.

A wata sanarwa, babban sakataren yada labarai na Gwamna Aiyedatiwa, Ebenezer Adeniyan, ya ce ba za a biya mataimakan daga asusun gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa na shirin ɗage dakatarwan da ta yi wa Sanata Abdul Ningi, ta faɗi dalili

Adeniyan ya ce kwamishinan ya yi naɗe-naɗen ba tare da sahalewar Gwamna Aiyedatiwa ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Tinubu zai shilla zuwa birnin Dakar

A wani rahoton na daban kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu zai shilla zuwa Dakar, babban birnin ƙasar Senegal domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban ƙasa

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu zai yi wannan tafiya zuwa Senegal kuma ya dawo gida Najeriya a ranar 2 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262