Muhimman Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani Game da Shugaba Tinubu Yayin da Ya Cika Shekara 72
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, shugaban Najeriya na yanzu, ya yi bikin cika shekaru 72 da haihuwa a ranar Jumu'a, 29 ga Maris, 2024.
Idan baku manta ba a kwanakin baya Shugaban Ƙasa Tinubu ya sanar da soke dukkan wani nau'i na biki ko taya murna a ranar da ya ƙara shekara, rahoton Tribune.
A wannan lokaci na bikin cikarsa shekaru 72 a duniya, Legit Hausa ta tattaro muku abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Shugaba Tinubu, ga su kamar haka:
1. Mahaifarsa
An haifi Bola Ahmed Tinubu ne a jihar Osun, ɗaya daga cikin jihohin da ke shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Karatunsa
Tinubu ya yi karatu a Ibadan, Legas, da jami’ar jihar Chicago, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin Akanta a shekarar 1979.
3. Tarihin ayyukan da ya yi
Shugaba Tinubu ya yi aiki a kamfanoni daban-daban na akantan kudi a Amurka kafin ya dawo kamfanin Mobil Oil Nigeria kuma daga karshe ya zama ɗan siyasa.
4. Yadda ya faro siyasa
Tinubu ya fara harkar siyasa ne tun a shekarun 1990, inda ya samu nasarar zama sanata karkashin inuwar Social Democratic Party (SDP), daga bisani ya zama jigo a siyasar Najeriya.
5. Sanatan Legas ta Yamma
Bola Tinubu ya riƙe kujerar Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma daga ranar 5 ga Disamba, 1992, zuwa ranar 17 ga Nuwamba, 1993, karo na farko da ya fara siyasa a majalisa.
6. Gwamnan Legas
Ya yi gwamnan jihar Legas karo biyu a jere daga 1999 zuwa 2007 a karkashin inuwar jam’iyyar Alliance for Democracy (ADC).
7. Zama shugaban Najeriya
Ƙasa ɗa shekara ɗaya da ta wuce, Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya bayan ƴa doke manyan abokan hamayya kamar Atiku Abubakar da Peter Obi.
A ranar 29 ga watan Mayu, 2023 Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasa na 16 a Najeriya.
8. Rayuwar iyalinsa
Duk da kasancewarsa mabiyin addidim Musulunci, Bola Ahmed Tinubu ya auri Remi Tinubu, wadda ta kai muƙami babba a addinin kirista. Oluremi da Bola Tinubu suna da yara hudu.
9. Kasuwanci
Tinubu babban ɗan kasuwa ne da ya shiga harkokin kasuwanci daban-daban, inda ya yi aiki a babban kamfani kuma yana da hannayen jari a kamfanoni da dama.
10. Jagoran yarbawa
A matsayin babban jigo a cikin kabilar Yarbawa, shugabancin Tinubu ya wuce siyasa kaɗai, yana da tasiri a fannin al’adu da zamantakewa.
FG ta bada tallafin aikin hajji
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu ta tallafawa aikin hajjin bana da N90bn domin ragewa alhazai tsadar kuɗin kujera.
Wata majiya daga hukumar NAHCON ta bayyana cewa wannan tallafin ne ya sa aka nemi alhazai su cika N1.9m amma da sai ƙarin ya wuce haka.
Asali: Legit.ng